APC ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Omo-Agege

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC a Jihar Delta ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, daga zama mamban jam’iyyar kan zargin yi wa jam’iyya zagon ƙasa da sauran laifuka da ba a bayyana su ba.

APC reshen Delta ta sanar da koran Omo-Agage daga jam’iyyar ce cikin wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Maris, 2023 wadda aka raba wa manema labarai a ranar Litinin.

Idan ba a manta ba, Omo-Agege ya yi takarar gwamnan jihar Delta ƙarƙashin APC inda ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar PDP, Sheriff Oborevwori a zaɓen da ya gudana kwanan baya.

Cikin wasiƙar mai ɗauke da sa hannu Shugaban Jam’iyyar na jihar, Ulebor Isaac, a madadin Kwamitin Shugabannin APC na jihar da Sakatarenta, Inana Michael, da sauran mutum 23, suka yanke korar Omo-Agege daga jam’iyyar a matsayin ɗan jam’iyyar a reshen Gundumar Orogun da Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Arewa.

A cewar wasiƙar, “A taron da Kwamitin Shugabannin APC na Jihar Delta ya gudanar a ranar 31 ga Maris, 2023 a Sakatariyar jam’iyyar da ke Asaba…

“….daidai da tanadin Doka ta 21.2 (1)(II)(VII) 21.3 da 21.5(g) na kundin tsarin mulki na 2022 (wanda aka yi wa gyara) mun yi ittifaƙin kan korar Sanata Omo Agege a matsayin mamba a jam’iyyar.”

Wasiƙar ta nuna an ɗauki wannan mataki a kan Ovie Omo Agege ne saboda yi wa jam’iyya zagon ƙasa gami da sauran laifukan da ba a bayyana ba.

Haka nan, ta ce korar ta fara aiki ne nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *