Matar Sanata Kalu, Ifeoma Kalu ta rasu

Daga WAKILINMU

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya ba da sanarwar mutuwar matarsa, Mrs Ifeoma Kalu.

Marigayiyar ta bar duniya tana da shekara 61.

Sanata Kalu ya sanar da mutuwar matar tasa ne a shafinsa na soshiyal midiya.

“Zuciya cike da alhini da jimami muke sanar da mutuwar Mrs Ifeoma Ada Kalu tana da shekara 61.

“Mutumiyar kirki ce a halin rayuwarta, kuma mai himma wajen bautar Allah da hidimta wa al’umma.

“Za a gudanar da ibadar tunawa da ita a Amurka,” in sanarwar.

Kalu ya buƙaci al’umma da su tuna da marigayiyar cikin addu’o’insu a wannan lokaci na mawuyacin hali.