Siyasa

Farfesa Alkali ya ajiye muƙaminsa na shugaban Jam’iyyar NNPP

Farfesa Alkali ya ajiye muƙaminsa na shugaban Jam’iyyar NNPP

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar NNPP na Ƙasa, Farfesa Rufai Alkali, ya yi murabus daga muƙaminsa a matsayin shugaban jam'iyyar. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar Alkali ya miƙa wasiƙar ajiye muƙamin nasa ne ga Sakataren jam'iyyar da nufin bai wa sabbin hannu shigowa don ɗorawa daga nasarorin da suka samu cikin taƙaitaccen lokacin da ya yi riƙe da jam'iyyar. Ya ce, ”Ina mai sanar da kai zan ajiye muƙamina a matsayin Shugaban Jam'iyyar NNPP na Ƙasa sannan in koma gefe daga ranar Juma'a, 31 ga Maris, 2023. “Bisa la'akari da yadda harkoki suka gudana kafin da bayan babban…
Read More
PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu ƙusoshinta

PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu ƙusoshinta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar PDP na Ƙasa (NWC) a ranar jiya Alhamis, ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu jiga-jiganta. Mambobin da aka soke dakatarwarsu sun haza da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose; Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim; Farfesa Dennis Ityavyar, Dakta Aslam Aliyu da Ibrahim Shema. Hakan na cikin wata sanarwar ne mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar na ƙasa, Debo Ologunaba. Ya ce, an ɗauki matakin hakan ne yayin taron na NWC a ranar Alhamis, inda mamabobin jam'iyyar suka yi tattaunawa mai zurfi kan abubuwan da…
Read More
Zargin gwamnatin riƙon ƙwarya: Jam’iyyu sun nemi a yi ’yar ƙure

Zargin gwamnatin riƙon ƙwarya: Jam’iyyu sun nemi a yi ’yar ƙure

*PDP da APC na son DSS ta kama sunaye*Cikin LP ya ɗuri ruwa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan tawagar ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyun APC da PDP sun ƙalubalanci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kamo kuma ta bayyana masu shirya gudanar da gwamnatin riƙon ƙwarya a Nijeriya. Majalisar a wata tattaunawa daban-daban da jaridun Nijeriya a ranar Laraba, 29 ga Maris, 2023, a Abuja, ta ce yunƙurin gudanar da gwamnatin riƙon ƙwarya ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar, inda ta ce, ya kamata a gano waɗanda suka shirya maƙarƙashiyar (sunansu) tare…
Read More
Raɗɗa ya karɓi shaidar lashe zaɓen gwamnan Katsina

Raɗɗa ya karɓi shaidar lashe zaɓen gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC, ta ba wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa takardar shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar a ranar Alhamis. Kwamishinan hukumar zave mai wakiltar Jihohin Kano, Katsina da Jigawa, Farfesa A. A Zuru ne ya miƙa shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓen gwamnan da mataimakinsa da kuma 'yan majalisar dokoki na jihar su 31. Da yake jawabi, Dr. Dikko Raɗɗa, ya gode wa Allah bisa nasarar da ya samu na lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023. Ya kuma yaba wa hukumar zaɓe mai…
Read More
HOTUNA: Yadda masoya suka yi dandazo wurin karɓar shaidar lashe zaɓen Abba Kabir

HOTUNA: Yadda masoya suka yi dandazo wurin karɓar shaidar lashe zaɓen Abba Kabir

A ranar Laraba Hukumar INEC ta miƙa wa 'yan takarar da suka lashe zaɓen gwamna a jihohinsu shaidar lashe zaɓen gwamnan da ya gudanar ranar 18 ga Maris, 2023. Haka ma lamarin ya kasance a Jihar Kano, inda ɗan takarar Jam'iyyar NNPP, Abba Kabir da Mataimakinsa, Aminu Abdussalam, suka karɓi shaidar lashe zaɓe a matsayin gwamna da mataimakinsa daga hannun INEC. Masoya daga sassan jihar suka fito don nuna goyon baya da murnar ga Gwamnan Kano mai jiran gado da mataimakinsa yayin da suka karɓi shaidar lashen zaɓen. Ga ƙarin hotunan irin wainar da aka toya daga Sani Maikatanga:
Read More
Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna a jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya taya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, murna. Ta cikin wani sako na murya da mai magana da yawunsa, Hassan Musa Fagge, ya saki a manhajar WhatsApp a ranar Laraba, Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida addu’ar Allah Ya sa ya zama shugaba nagari. A cewar Gawuna, tun bayan da hukumar zaɓe, INEC, ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen, jam’iyyar APC…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Abba Kabir ya karɓi shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Da Ɗumi-ɗumi: Abba Kabir ya karɓi shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Jihar Kano, ta miƙa wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar ƙarƙashin jam'iyyar NNPP shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar. Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Abdulsalam Gwarzo sun karbi satifiket ɗin ne ranar Laraba a babban ofishin INEC da ke Kano. Cikin waɗanda suka halarci taron miƙa shaidar, akwai Shugaban hukumar zaben na Kano, Ambasada Zango Abdu, Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda da dai sauran jiga-jigan jam'iyyar NNPP na ciki da wajen jihar.
Read More
Abba Gida-gida ya gayyaci al’umma zuwa shaida karɓar shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Abba Gida-gida ya gayyaci al’umma zuwa shaida karɓar shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci al'ummar jihar Kano da kewaye zuwa inda Hikunar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, za ta miƙa masa shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano tare da mataimakinsa, Kwamred Abdulsalam Gwarzo. Ranar Laraba ake sa ran INEC za ta miƙa wa waɗanda suka lashe zaɓen gwamna a jihohinsu shaidar lashe zaɓen. Gayyatar Abba Gida-gida na ƙunshe ne cikin sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata. Sanusi Bature ya ce gangamin karɓar shaidar zai gudana ne…
Read More
INEC ta tsayar da ranar gudanar da zaɓen Adamawa da sauransu

INEC ta tsayar da ranar gudanar da zaɓen Adamawa da sauransu

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta tsayar da ranar da za ta gudanar da zaɓen gwamnan da na majalisar tarayya da na jihohi a wuraren da zaɓe bai kammala ba. INEC ta ce ya zuwa ranar 15 ga Afrilun 2023 za ta gudanar da zaɓe a wuraren da lamarin ya shafa. Hukumar ta bayyana hakan ne ta shafinta na Tiwita a ranar Litinin. “Bayan taro da aka yi yau, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta yanke gudanar da dukkan zaɓukan gwamna, na 'yan majalisar tarayya da na jihohi da suka yi saura a ranar Asabar, 15 ga Afrilun 2023. “Ƙarin bayani…
Read More
Matawalle ya amsa shan kaye kuma ya nemi afuwar mutanen Zamfara

Matawalle ya amsa shan kaye kuma ya nemi afuwar mutanen Zamfara

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara ya amsa shan kaye a zaɓen da aka kammala tare kuma da neman afuwa. Ɗan takatar Jam'iyyar PDP Dauda Lawal Dare ne ya kayar da gwamnan. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani saƙon murya da ya fitar ga 'yan jihar, inda ya ce shi da magoya bayansa sun karɓi ƙaddara. Ya ce lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, ya zauna tare da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar wajen ganin an samo hanyoyin dawo da zaman lafiya ta…
Read More