Siyasa

PDP ta sake tsunduma cikin rikici, ta dakatar da wasu jiga-jiganta

PDP ta sake tsunduma cikin rikici, ta dakatar da wasu jiga-jiganta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga-jigan mambobinta da suka haɗa da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Pius Anyim, Farfesa Dennis Ityavyar da Aslam Aliyu, bisa zargin katsalandan a harƙallar jam'iyyar. Bayanin Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Mista Debo Ologunagba, a ranar Alhamis. Sanarwar ta kuma cigaba da cewa, “Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na Jam’iyyar PDP ya yi nazari sosai kan al’amuran jam’iyyarmu a ƙasar nan da kuma bin tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin PDP (kamar yadda aka…
Read More
2023: Gwamnoni 17 sabbin yankan rake – 9 ’yan tazarce – 2 ’yan jiran tsammani

2023: Gwamnoni 17 sabbin yankan rake – 9 ’yan tazarce – 2 ’yan jiran tsammani

Daga SANI AHMAD a Abuja A ranar Asabar, wacce ta zo daidai da 18 ga Maris, 2023, ne aka gudanar da zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisun dokokin Nijeriya bayan kusan kammala wa’adin mulkinsa na yanzu. An gudanar da zaɓukan gwamnonin a jihohi 28, yayin da sauran takwas kuma aka gudanar da na majalisun dokokin jihohin tare da na jihohin 28. Ma’ana; an yi zaɓen ’yan majalisar dokokin jihohin Nijeriya 36 bakiɗaya, amma a jihohi 28 ne kawai aka yi na gwamnoni. Wannan ya biyo bayan wasu hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli ne da ya shafi zangon mulkin wasu jihohi ne, waɗanda…
Read More
Kotu ta tabbatar da Adeleke Gwamnan Osun

Kotu ta tabbatar da Adeleke Gwamnan Osun

Daga WAKILINMU Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin Gwamnan Jihar Osun. Tun bayan zaɓen gwamna da ya gudana a jihar ranar 16 ga Yulin bara, ɗan takarar jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya tafi kotu inda ya ƙalubalanci nasarar da Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya samu yayin zaɓen. A ranar Juma'a, Kotun Ƙolin ƙarƙashin Mai Shari'a Mohammed Shuaibu, ta yanke hukunci kan shari'ar inda ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamnan jihar.
Read More
Zaɓen Peter Obi

Zaɓen Peter Obi

Daga MUHAMMAD M. MUSTAPHA A matakin farko, bayan Hijirarsa zuwa garin Madina Haskakkiya, Annabi Muhammadu SAW ya rubuta yarjejeniyar zamantakewa, don tabbatar da zaman lafiya da lumana. Ya zo a cikin wannan yarjejeniya, kamar yadda Malam Ibnu Hisham ya bayyana a littafinsa Assirah Annabawiyya, cewa: 'tabbas Yahudawan Banu Auf al'umma ɗaya ne tare da Muminai, Yahudawa su yi addininsu Musulmi ma su yi addininsu. Haka Yahudawan Banun Najar, Banul Haris, Banu Sa'idah…..duk al'umma ɗaya ne tare da Muminai'. Hakana wannan yarjejeniya ta ci gaba da bayanin haɗaka ta taimakekeniyar rayuwa a tsakanin wannan al'umma ɗaya masu mabanbantan addinai: kowa a…
Read More
APC a Jihar Adamawa ta dakatar da Boss Mustapha kan zargin ƙin taimaka wa Binani lokacin zaɓe

APC a Jihar Adamawa ta dakatar da Boss Mustapha kan zargin ƙin taimaka wa Binani lokacin zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, saboda ya sha ƙasa a hannun Jam’iyyar PDP a lokacin zaɓukan da suka gabata. Jam’iyyar ta ce Boss Mustapha bai bayar da gudunmawar nasarar da ’yan takarar Shugaban Ƙasa da na Gwamna na APC suka samu a lokacin da ake buƙatar taimakonsa ba. Da yake sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Yola, babban birnin Jihar, Shugaban gundumar Gwadabawa, Mu’azu Kabiru, ya ce Boss Mustapha bai jajirce wajen samun nasarar APC ba a zavukan. Ya ce bisa wasu ƙorafe-ƙorafe…
Read More
Alex Otti ya ci zaɓen Gwamnan Abia

Alex Otti ya ci zaɓen Gwamnan Abia

Daga BASHIR ISAH Dokta Alex Otti na Jam’iyyar Labour ya lashe zaɓen Gwamna a Jihar Abia. Otti ya samu wannan nasarar ce bayan da ya kere sauran abokan takararsa yawun ƙuri’u a zaven da ya gudana a jihar ranar Asabar da ta gabata. Shi ne ya zo na ɗaya da ƙuri’u 175, 467, yayin da Okey Ahiwe na Jam’iyyar PDP ke bi masa da ƙuri’u 88,529. Baturen zaɓen, Farfesa Nnenna Oti, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen a hedikwatar hukumar INEC Umuahia, babban birnin jihar. Ga qarin bayani game da sakamakon kamar haka: (1) Aba ta Arewa APC – 487APGA…
Read More
Peter Mbah ya lashe zaɓen Gwamnan Enugu

Peter Mbah ya lashe zaɓen Gwamnan Enugu

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana ɗan takarar gwamnan na Jam’iyyar PDP a Enugu, Peter Mbah, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a jihar ranar Asabar da ta gabata. INEC ta ce Mbah ya cinye zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’u 160,895. Xan takarar Jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, shi ne ya zo na biyu da quri’u 157,552, yayin da Uche Nnaji na Jam’iyyar APC ya zo na uku da ƙuri’u 14,575. Baturen zaɓen, Farfesa Maduebibisi Ofo-Iwe, shi ne wanda ya bayyana sakamakon zaɓen.
Read More
APC ta buƙaci a soke zaɓen gwamnan Kano

APC ta buƙaci a soke zaɓen gwamnan Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Jam’iyyar APC a Jihar kano ta yi fatali da zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar ɗin da ta gabata, tare da neman hukumar zaɓe, INEC, ta soke zaɓen. Shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan lokacin taron manema labarai wanda ya gudana a ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar da ke cikin birnin a ranar Larabar. Abdullahi Abbas wanda mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Barr. Abdul Adamu Fagge ya wakilta, ya ce zaɓen da aka gudanar a ranar Aasabar, 18 ga watan Maris akwai kura-kurai…
Read More
APC ta ci zaɓen gwamna a Neja

APC ta ci zaɓen gwamna a Neja

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar gwamna ƙarƙashin Jam'iyyar APC a jihar Neja, Mohammed Umar-Bago, shi ne ya lashe zaɓen da ya guda a jihar Asabar da ta gabata. Bago, wanda ɗan Majalisar Wakilai mai ci ne mai wakiltar mazaɓar Chanchaga, ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 469,896, in ji INEC. Baturen zaɓen, Clement Alawa, ya ce an tabbatar da Bago a matsayin wanda ya ci zaɓen ne bayan cika duka sharuɗɗan da suka dace. Alhaji Isah Liman Kantigi na Jam'iyyar PDP shi ne ya rufa wa Bago baya da ƙuri'u 387,476, in ji Mr Alawa.
Read More
Zaɓen gwamna a Katsina cike yake da maguɗi – Lado

Zaɓen gwamna a Katsina cike yake da maguɗi – Lado

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Ɗan Marke, ya yi watsi da sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta bayyana. Cikin wata hira da ya yi da BBC, Sanata Lado, ya ce, zaɓe ne mai cike da maguɗi da aringizon ƙuri'u da barazana ga masu zaɓe, da dai duk wani ha'incin da bai taɓa gani a harkar zaɓe ba. Ya ce, "Ba mu gamsu da wannan sakamakon zaɓen ba tun da mun san ba abin da al’umma suka zaɓa ba ne aka bayyana.” Ɗan takarar ya…
Read More