Kotu ta tabbatar da Adeleke Gwamnan Osun

Daga WAKILINMU

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin Gwamnan Jihar Osun.

Tun bayan zaɓen gwamna da ya gudana a jihar ranar 16 ga Yulin bara, ɗan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya tafi kotu inda ya ƙalubalanci nasarar da Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu yayin zaɓen.

A ranar Juma’a, Kotun Ƙolin ƙarƙashin Mai Shari’a Mohammed Shuaibu, ta yanke hukunci kan shari’ar inda ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamnan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *