2023: Gwamnoni 17 sabbin yankan rake – 9 ’yan tazarce – 2 ’yan jiran tsammani

Daga SANI AHMAD a Abuja

A ranar Asabar, wacce ta zo daidai da 18 ga Maris, 2023, ne aka gudanar da zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisun dokokin Nijeriya bayan kusan kammala wa’adin mulkinsa na yanzu.

An gudanar da zaɓukan gwamnonin a jihohi 28, yayin da sauran takwas kuma aka gudanar da na majalisun dokokin jihohin tare da na jihohin 28. Ma’ana; an yi zaɓen ’yan majalisar dokokin jihohin Nijeriya 36 bakiɗaya, amma a jihohi 28 ne kawai aka yi na gwamnoni. Wannan ya biyo bayan wasu hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli ne da ya shafi zangon mulkin wasu jihohi ne, waɗanda a na tsaka muliki, sai kotun ta soke zaɓen gwamnan.

Haka nan a jihohi 17 ne suka samu sababbin gwamnoni, yayin da gwamnoni tara suka samu damar yin tazarce, inda kuma kawo yanzu ba a iya kammala zaɓukan a jihohi biyu ba.

Blueprint Manhaja ta tattaro bayanan yadda cikakken sakamakon zaɓukan ya kasance kamar haka:

Jerin sababbin gwamnonin da aka zaɓa:

Kano (NNPP)
Hukumar Zave INEC, ta tabbatar da ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Abba ya taki wannan matsayi ne bayan da ya samu ƙuri’u 1,019,602 wanda hakan ya ba shi damar doke babban abokin hamayyarsa na APC kuma Mataimakin Gwamnan jihar mai ci, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya tsira da ƙuri’u 890,705 a zaɓen.

INEC ta ce Muhammad Sani Abacha na Jam’iyyar PDP, shi ne ya zo na uku da ƙuri’u 15,957.

Da safiyar Litinin INEC ta ayyana Abba sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Kano mai jiran gado.

Wani ala’amari mai ɗaukar hankali da Manhaja ta gano game da nasarar da Abba ya samu, shi ne yadda ƙananan yara da sauran mata a jihar suka mamaye tituna suna nuna murnarsu.

Kaduna (APC)

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana ɗan takarar Jam’iyyar APC, Uba Sani, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar Kaduna a zaɓen 2023.

Jami’in da ya sanar da sakamakon zaven, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis ya ce Sani ya samu ƙuri’u dubu 730,002 inda ya doke abokin takararsa, Isa Ashiru na Jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u dubu 719,196.

Bilbis, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗanfodio da ke Sakkwato, ya ce xan takarar Jam’iyyar Labour, Jonathan Asake, ya zo na uku bayan ya samu ƙuri’u dubu 58,283.

Ya ƙara da cewa ɗan takarar Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Suleiman Hunkuyi, ya samu ƙuri’u dubu 21,405 inda ya zama na huɗu a zaɓen.

Katsina (APC)

Hukumar Zaven Nijeriya INEC ta ayyana Dokta Umar Radda na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina.

Radda ya samu nasara ne da ƙuri’u 859,892, yayin da mai biye masa Garba Yakubu Lado Danmarke na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’a 486,620.

Jami’in da ke tattara sakamakon zaɓen gwamnan a jihar ta Katsina, Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau ne ya bayyana sakamakon a daren Lahadi.

Zamfara (PDP)

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Zamfara ta bayyana Dauda Lawal Dare a matsayin wanda ya lashe zaven gwamnan jihar.

Dauda Lawal ya samu ƙuri’u 377,726, inda ya yi nasara a kan gwamna mai ci Bello Muhammad Matawalle wanda ya samu ƙuri’u 311,976.

An dai kwashe tsawon lokaci ana tattara sakamakon zaɓen sanadiyyar jinkiri da aka samu.

Rahotanni da suka fito daga jihar sun ce an sace jami’an tattara sakamakon zaɓe a kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin jihar, daga ƙaramar hukumar Maradun.

Abia (LP)

Dokta Alex Otti na Jam’iyyar Labour ya lashe zaɓen Gwamna a Jihar Abia.

Otti ya samu wannan nasarar ce bayan da ya kere sauran abokan takararsa yawun ƙuri’u a zaɓen da ya gudana a jihar ranar Asabar da ta gabata.

Shi ne ya zo na ɗaya da ƙuri’u 175, 467, yayin da Okey Ahiwe na Jam’iyyar PDP ke bi masa da ƙuri’u 88,529.

Baturen zaɓen, Farfesa Nnenna Oti, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen a hedikwatar hukumar INEC Umuahia, babban birnin jihar.

Inugu (PDP)

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana ɗan takarar gwamnan na Jam’iyyar PDP a Enugu, Peter Mbah, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a jihar ranar Asabar da ta gabata.

INEC ta ce Mbah ya cinye zaven ne bayan da ya samu ƙuri’u 160,895. Ɗan takarar Jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, shi ne ya zo na biyu da quri’u 157,552, yayin da Uche Nnaji na Jam’iyyar APC ya zo na uku da ƙuri’u 14,575.

Baturen zaven, Farfesa Maduebibisi Ofo-Iwe, shi ne wanda ya bayyana sakamakon zaɓen.

Neja (APC)

Ɗan takarar gwamna ƙarƙashin Jam’iyyar APC a jihar Neja, Mohammed Umar-Bago, shi ne ya lashe zaɓen da ya guda a jihar Asabar da ta gabata.

Bago, wanda ɗan Majalisar Wakilai mai ci ne mai wakiltar mazaɓar Chanchaga, ya lashe zaven ne da ƙuri’u 469,896, in ji INEC.

Baturen zaɓen, Clement Alawa, ya ce an tabbatar da Bago a matsayin wanda ya ci zaɓen ne bayan cika duka sharuɗɗan da suka dace.

Alhaji Isah Liman Kantigi na Jam’iyyar PDP shi ne ya rufa wa Bago baya da ƙuri’u 387,476, in ji Mr Alawa.

Sakkwato (APC)

Ɗan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a Sakkwato, Aliyu Ahmed Sokoto, ya lashe zaɓen gwamanan jihar da ƙuri’u 453,661.

Aliyu ya doke babban abokin hamayyarsa na PDP, Umar Saidu Ubandoma, wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 404,632.

Delta (PDP)

Hukumar INEC ta bayyana Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Delta.

Wannan ya kasance bisa ga sakamakon da aka sanar a ranar Litinin, Maris 20, 2023, ta Monday Udoh-Tom, Kwamishinan Zaɓen jihar.

Udoh-Tom ya ce, Oborevwori ya lashe qananan hukumomi 21 cikin 25 da aka haɗa a jihar inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Ovie Omo-Agege.

Oborevwori ya samu ƙuri’u 360,234, Omo-Agege ya samu ƙuri’u 240,229, yayin da ɗan takarar jam’iyyar APGA, Chief Great Ogboru ya samu ƙuri’u 11,029.

A cikin ƙananan hukumomi 25 da ke jihar, Oborevwori na PDP ya samu nasara a 21 daga cikinsu, Omo-Agege na APC ya lashe sauran ƙananan hukumomi huɗu.

Filato (PDP)

Hukumar Zaɓen Nijeriya ta ayyana Caleb Mutfwang, na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Filato.

Baturen zaven Musa Yusuf ya ce Mutfwanhg ne wanda ya samu ƙuri’u mafi yawa, 525,299 inda ya doke babban abokin karawarsa na Jam’iyyar APC, Nantawe Yilwatda da ya samu ƙuri’u 481,370.

Ɗan takarar na PDP ya bai wa abokin hamayyarsa na APC tazarar ƙuri’u 43,929. PDP ta lashe zaɓe a ƙananan hukumomi 10 yayin da APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi bakwai.

Kuros Ribas (APC)

Prince Bassey Edet Otu ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar Kuros Ribas tare da sauran jihohi a ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Hukumar Zave ta Nijeriya INEC, ce ta bayyana ɗan takarar Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma ya kayar da abokin burminsa na Jam’iyyar PDP Sunday Onor.

Ɗan takarar ya samu nasarar da ƙuri’u 258,619 kan abokin hamayyarsa da ƙuri’a 179,636.

Ebonyi (APC)

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta bayyana ɗan takarar APC na Jihar Ebonyi Francis Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban da ke tattara sakamakon Farfesa Charles Igwe, Nsukka shi ne ya bayyana Francis Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaven, bayan cika duka sharuɗan da ake tsammani ya cika.

Francis Nwifuru ya lashe ƙananan hukumomi 10 cikin 13 da ake da su a jihar, yayin da ɗan takarar APGA ya lashe biyu na PDP ya lashe 1.

Shi ne zai zama gwamna na huɗu ga jihar ta Ebonyi da ba ta fi shekara 27 da ƙirƙira ba.

Jigawa (APC)

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa kuma ɗan takarar gwamnan jihar a Jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Umar Namadi ya lashe zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ranar Asabar.

Namadi ya lashe zaɓe a ƙananan hukumomi 26 daga cikin 27 na jihar.

Ya samu ƙuri’u 618,449 inda ya samu galaba a kan ‘yan takarar Jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido da kuma NNPP Aminu Ibrahim wanda ya zo na uku.

Ɗan takarar PDP ya samu ƙuri’u 368,726 a yayin da ɗan takarar NNPP ya samu ƙuri’u 37,156.

Babban jami’in da ke kula da zaɓen, Farfesa Zaiyanu Umar ne ya sanar da sakamakon zaɓen a ranar Lahadi.

Taraba (PDP)

INEC ta bayyana ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Taraba, Laftanar Kanar Agbu Kefas (mai ritaya) a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Kefas ya samu ƙuri’u  236,712, inda ya doke ‘yan takarar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da All Progressives Congress (APC), inda ɗan takarar ya zo na uku.

Benuwai (APC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Qasa (INEC), ta bayyana Fr. Hycinth Alia na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Benuwai.

Jami’in Zaɓe na INEC, Farfesa Farouk Kuta, wanda kuma shine Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya dake Minna ne ya bayyana sakamakon zaɓen a Makurdi a ranar Litinin.

Ya ce Alia ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 473,933 inda ya doke abokin hamayyarsa Titus Uba na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 223,913.

Jami’in zaɓen ya ce duk da cewa zaɓen bai gudana a ƙaramar hukumar Kwande ba, amma bambancin ƙuri’u tsakanin Alia da ɗan takarar PDP ya kai 251,020.

Akwa Ibom (PDP)

Hukumar Za e ta Nijeriya (INEC), ta bayyana ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom Fasto Umo Eno a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka kammala.

Eno ya samu ƙuri’u 354,548 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Sanata Bassey Akpan wanda ya samu ƙuri’u 136, 262. Ɗan takarar Jam’iyyar APC ya zo na uku da quri’u 129,602.

Eno ya lashe ƙananan hukumomi 29 yayin da dan takarar jam’iyyar YPP Sanata Bassey Akpan ya lashe ƙaramar hukumarsa ta Ibiono Ibom da ƙananan hukumomin Ikono.

Ribas (PDP)

Hukumar Zaɓe ta Nijeriya INEC, ta bayyana ɗan takarar Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ribas wanda aka gudanar ranar Asabar.

Sim Fubara ya samu ƙuri’u 302,614, inda ya lashe zaɓen jihar, INEC ta bayyana a hukumance a ranar Litinin ɗin da ta gabata bayan tattara sakamako daga dukkan ƙananan hukumomin a hedikwatarta da ke Fatakwal.

Wanda ya zo na biyu a zaɓen, Tonye Cole na Jam’iyyar All Progressives Congress ya samu ƙuri’u 95,274 yayin da Beatrice Itubo ta Jam’iyyar Labour ta samu ƙuri’u 22,224 ta zo na uku.

Jerin gwamnonin da suka yi tazarce:

Legas

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓe na jihar Legs, Professor Adenike Temidayo Oladiji ya bayyana gwamna ma ci Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya samu nasarar komawa kan mulki karo na biyu. Sanwo Olu ya samu nasara ne da ƙuri’u 762,134.

Gombe

A jihar Gombe ma, hukumar zave ta hannun jami’ar tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Maimuna Waziri ta ayyana Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya yi nasarar sake ɗarewa kan mulki da ƙuri’u 345,821.

Kwara

Hukumar zave a jihar Kwara, ta ayyana gwaman mai ci AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya samu nasara a zaven gwamna.

AbdulRahman ya koma kan mulki ne bayan samun nasara a illahirin kananan hukumomi 16 na faɗin jihar.

Yobe

A Jihar Yobe ma, Gwamna Mai Mala Buni ne ya samu nasarar komawa kan karagar mulki.

Mai Mala Buni ya samu nasara ne da kuri’u 317,113, inda ya doke abokin karawarsa Sheriff Abdullahi na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 104,259.

Borno

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jam’iyyar APC ya sake lashen zaɓen gwamnan Jihar Borno a karo na biyu 

Da yake bayyana sakamakon da yammacin Litinin, Baturen zaɓen, Jude Rabo, ya ce ɗan takarar jam’iyyar APC, Babagana Zulum, shi ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 545,542.

Yayin da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Mohammed Jajari ya samu ƙuri’u 82,14

Oyo

Gwamna Seyi Makinde na Jam’iyyar PDP, shi ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Makinde wanda shi ne gwamna mai ci ya samu quri’u mafi yawa inda ya bai wa babban ɗan adawa a jihar, Teslim Folarin na Jam’iyyar APC tazarar ƙuri’u kusan dubu 300.

Ogun

A can jihar Ogun ma, Gwamna Dapo Abiodun ne ya ci zaɓen gwamnan jihar da da aka yi a ranar Asabar.

Ya samu nasara a karo na biyu ne bayan samun ƙuri’u 276,298, inda ya doke abokin hamayyarsa Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 262,383.

Nasarawa

A jihar Nasarawa ma, hukumar zaɓe ta sanar da gwamna mai ci Abdullahi Sule a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar.

Jami’in tattara sakamako zaɓen gwamnan jihar Ishaya Tanko, shi ya sanar da hakan a Lafiya babban birnin jihar.

Abdullahi Sule ya samu damar komawa kan karagar mulki ne da kuri’u 347,209.

Bauchi

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya sake ɗarewa kan mulki karo na biyu a sakamakon zaɓen gwamna da aka sanar a ranar Litinin.

Jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya ce Bala ƙaura ya samu nasara ne da ƙuri’u 525,280.

Ya doke babban abokin hamayyarsa Air Marshal Abubakar Sadique Baba na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 432,272.

Jihohin da zaɓe bai kammalu ba:

Kebbi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi ta bayyana sakamakon zaɓen gwamna na ƙananan hukumomi 20 na jihar bisa ga sakamakon da aka samu 388, 258 da 342, 258 da jam’iyyu biyu da suka fi kowa a zaɓen suka kaɗa ƙuri’a.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Yusuf Saidu na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato ya ce “Mun lura da inda aka soke sakamakon zaɓen, kuma ya nuna cewa an soke zaɓen a ƙananan hukumomi 20 na jihar daga cikin ƙananan hukumomi 21. 

Adamawa

Baturen Zaɓe na INEC a Jihar Adamawa ya bayyana cewa zaven jihar bai kammalu ba, inda ya ce akwai buƙatar sake gudanar da zave a wasu mazaɓun.

Ya ce, ba za a ayyana wanda ya ci zaɓe ba, har sai an gudanar da zaɓe a wasu mazaɓu 47 daban-daban da ke qananan hukumomin jihar 21.

Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP na kan gaba da yawan ƙuri’u, inda Sanata Aisha Binani ta jam’iyya mai mulkin ƙasar wato APC ke biye masa.

Jihohin da ba a yi zaɓe ba:

Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Kogi, Ondo da kuma Osun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *