PDP ta sake tsunduma cikin rikici, ta dakatar da wasu jiga-jiganta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga-jigan mambobinta da suka haɗa da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Pius Anyim, Farfesa Dennis Ityavyar da Aslam Aliyu, bisa zargin katsalandan a harƙallar jam’iyyar.

Bayanin Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Mista Debo Ologunagba, a ranar Alhamis.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa, “Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na Jam’iyyar PDP ya yi nazari sosai kan al’amuran jam’iyyarmu a ƙasar nan da kuma bin tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin PDP (kamar yadda aka yi wa gyara a shekarar 2017), inda ya yanke hukunci da shi kan waɗannan mutane ga kwamitin ladabtarwa na ƙasa bisa rahotannin da ya bayar na yin sa-in-sa a cikin harƙallar jam’iyya.

“Hukumar Gudanarwar ta kuma amince da dakatar da waɗannan mutane daga jam’iyyar daga yau Alhamis, 23 ga Maris, 2023, da suka haɗa da Ayodele Fayose (Jihar Ekiti), Ayodele Fayose (Jihar Ekiti), Sanata Pius Anyim (Jihar Ebonyi), Dennis Ityavyar (jihar Benuwai), Dakta. Aslam Aliyu (Jihar Zamfara).

“PDP ta na kira ga dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da jiga-jigan jam’iyyarmu a faɗin ƙasar nan da su kasance cikin haɗin kai da mayar da hankali a wannan mawuyacin lokaci,” inji sanarwar.

Rahotannin sun nuna cewa, har yanzu ta tana-ƙasa-tana-dabo kan makomar Gwamnan Jihae Benuwe, Samuel Ioraer Ortom, da kuma na Jihar Ribas, Nyesom Wike, waɗanda su ma ake zargin su da yi wa jam’iyyar ta PDP zagon ƙasa da rashin biyayya, musamman a lokacin gudanar da Babban Zaɓen Ƙasa na 2023, wanda aka kammala shi a kwanan baya kaɗan.