Ramadan: Babu wani dalilin da zai sa ’yan kasuwa su riƙa ƙara farashi saboda azumi – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi ’yan kasuwar dake ƙara farashin kayayyaki saboda zuwan azumi da su daina saboda ya saɓa da koyarwar Musulunci.

Ya bayyana haka ne ranar Laraba, a cikin saƙonsa ga al’ummar Musulmi kan shiga watan Ramadan da aka fara ranar Alhamis.

Buhari, ya kuma shawarci Musulman Nijeriya da su yi amfani da lokacin wajen haskaka kyawawan ɗabi’un addinin Musulunci a mu’amalolinsu, ba wai kawai a baki ba.

Sanarwar, wacce Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, “Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen bayyana kyawawan ɗabi’un Musulunci irin su tausayi da ƙaunar juna.

“Wannan lokaci ne na komawa ga Allah da kuma jin tsoronSa, ta hanyar guje wa duk abin da zai cutar da ɗan Adam.

“Ramadan wata ne na kamewa daga barin ci da sha tun daga hudowar Alfijir har zuwa faɗuwar rana, kuma yana daidaita talaka da mai kuɗi a wajen jin yunwa, ta yadda kowa ke zama ɗaya.

“Ina sane da yadda wasu ’yan kasuwa ke ƙara farashin kayayyaki, ciki har da na kayan abinci, a kowanne watan Ramadan. Yin hakan ya saɓa da ainihin manufar azumin da ma ta Musulunci,” inji Buhari.

A ranar Alhamis ce Musulmin Nijeriya suka bi sahun takwarorinsu na sauran sassan duniya domin fara azumin watan Ramadan, bayan an ga watan a wurare da dama na ƙasar.