FIRS: Ma’aikata sun koka da rashin bin ƙa’ida wajen ƙarin matsayi

Daga AMINA YUSUF ALI

Ma’aikata a hukumar tattara haraji FIRS sun koka tare da nuna rashin gamsuwa a kan yadda aka gudanar da ƙarin muƙami a ma’aikatar.

Wani ma’aikaci a hukumar ya bayyana yadda mahukuntan hukumar suka kasa bin tsari wajen gudanar da ƙarin matsayi ga ma’aikatanta. 

Wannan ƙorafin yana qunshe ne a wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai ɗauke da jawabin ƙorafi wadda aka yi wa ministar kuɗi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed inda aka kira ta da ta shigo cikin maganar kuma ta taka wa mahukuntan burki a kan al’amarin. 

A cikin takardar ƙorafin ma’aikatan sun zargi mahukuntan FIRS da keta dokokin ɗaukar ma’aikata sun haifar da rashin cigaba da dankwafar da wasu ma’aikatan.

Ma’aikacin da ya yi rubutun ƙorafin ya bayyana cewa, ma’aikatar ba ta yi abinda ya dace ba wajen ƙara wa ma’aikatanta matsayia a ƙarin matsayin da ya gabata na 2022/2023.

A cewarsa, duk da jarrabawa da aka gudanar kuma wasu ma’aikatan sun lashe jarrabawar kuma sun cancanci muƙaman da suke nema, amma sai aka bar su a cikin tsammanin-wa-rabbuka.

Domin a cewar sa, ma’aikatar sai ta soke waccan jarrabawar ta kuma yi ƙarin matsayi ne kawai ga wasu tsirarun manyan daraktoci. Sannan ta nemi a sake wata jarrabawar bayan kwanaki 5. 

A don haka a cewar sa, suke ganin ya kamata ma’aikatar kuɗi a ƙarƙashin ministarta Zainab Shamsuna Ahmad ta sanya baki don kawo daidaito a lamarin.