Matawalle ya amsa shan kaye kuma ya nemi afuwar mutanen Zamfara

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara ya amsa shan kaye a zaɓen da aka kammala tare kuma da neman afuwa.

Ɗan takatar Jam’iyyar PDP Dauda Lawal Dare ne ya kayar da gwamnan. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani saƙon murya da ya fitar ga ‘yan jihar, inda ya ce shi da magoya bayansa sun karɓi ƙaddara.

Ya ce lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, ya zauna tare da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar wajen ganin an samo hanyoyin dawo da zaman lafiya ta hanyar tattaunawar zaman lafiya, inda ya ce har zuwa yau, babu abin da ya fi addabar jihar kamar rashin tsaro da ake fama da shi.

Matawalle ya ce baya ga tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindiga, ya kuma yi aiki tuƙuru wajen ganin gwamnatinsa ta kawo dukkan ɓangarorin siyasa zuwa ƙarƙashin inuwa ɗaya don zaman lafiya da haɗin kai ya wanzu a faɗin jihar.

Ya ce sun samu nasarar sasanta bangarorin siyasa da ba sa ɗasawa, wanda kuma shi ya buɗe hanyar gudanar da yaƙin neman zaɓe a jihar lami lafiya ba tare da wata matsala ba.