Majalisa za ta binciki ƙin amincewa da gyaran wasu sassan Kundin Tsarin Mulki da Buhari ya yi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Dattawan Nijeriya ta kafa wani kwamiti da zai binciki dalilin da ya sa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa da ƙuduri 19 cikin 35 na kundin tsarin mulkin ƙasar da majalisar ta miƙa masa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Talata, 21 ga watan Maris, 2022, ya bayyana hakan a jawabinsa yayin da ake ci gaba da zama bayan kammala zaɓen gwamna da na ’yan majalisun jihohi.

A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan wasu dokoki 16 na gyara kundin tsarin mulkin qasar daga cikin ƙudirori 35 da majalisar ta tara ta miƙa masa.

Lawan ya yaba wa Shugaba Buhari kan amincewa da wasu ƙudirori 16 na gyara kundin tsarin mulkin ƙasar, musamman ƙudurorin tabbatar da ’yancin cin gashin kan majalisun jihohi da na ɓangaren shari’a.

Sai dai ya ce, majalisar za ta tattauna da fadar shugaban ƙasa don fahimtar dalilin da ya sa ba a amince da sauran ƙudurorin 19 ba.