29
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Sanata Bola Tinubu ya gana da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu a gidan tsaro da ke Abuja. A wajen taron da aka gudanar a sirrance akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege; Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Iyiola Omisore da tsohon Sakataren Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugabancin Jam’iyyar APC, Hon James Faleke. A ƙarshen taron, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa ya ce taron wani aiki ne na yau da kullum. Ya ƙi bayyana batutuwan da aka tattauna…
