Siyasa

Zaɓen wannan karon ya ɗara wanda ya gabata inganci, in ji Sakkwatawa

Zaɓen wannan karon ya ɗara wanda ya gabata inganci, in ji Sakkwatawa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Yayin da harkokin zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi ke ci gaba da gudana, wasu 'yan ƙasa sun bayyana ra'ayoyinsu game da zaɓen. Ziyarar da wakilinmu ya kai a sassan birnin na Sakkwato, kusan bayanin duka ɗaya ne, inda masu jefa ƙuri'a suka nuna gamsuwarsu. Daga cikin waɗanda wakilin namu ya zanta da su, sun bayyana cewa an samu sauyi a zaɓen wannan karon idan aka kwatanta da zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata. A cewarsu, ingancin zaɓen wannan karon ya ɗara na wanda ya gabata.
Read More
INEC ta fara ɗora sakamakon zaɓe a intanet ta BVAS

INEC ta fara ɗora sakamakon zaɓe a intanet ta BVAS

Daga SANI AHMAD GIWA Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ɗora wasu daga cikin sakamakon zaɓen ranar Asabar ta hanyar BVAS. Rashin amfani da BVAS a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu ya haifar da dambarwar amincewa ga hukumar zaɓen, wanda ‘yan Nijeriya da jami’an zave suka yi kakkausar suka. Kodayake hukumar ta yi amfani da matsalar fasaha a matsayin dalilin rashin amfani da BVAS wajen watsa sakamako, da yawa masu suka sun ƙi amincewa da uzurin. Sai dai hukumar ta yi alƙawarin inganta tare da yin amfani da na'urar a zaɓen da ke gudana yau. Manhaja ta…
Read More
Matasa na yunƙurin hana zaɓe a Sakkwato

Matasa na yunƙurin hana zaɓe a Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gungun matasa na yunƙurin tada fitina yayin da ake shirin soma zaɓen gwamna da na ’yan majalisar dokoki a Jihar Sakkwato. Ma’aikatan zaɓe sun kwashe kayansu a rumfar zaɓe mai lamba 027 ta Aliyu Kyari kan hatsaniyar da matasa suka tayar suna masu cewar ba su yarda da a yi zaɓen ba. Tun da sanyin safiyar wannan Asabar ɗin dai matasa maza da mata suka fara shiga layi yayin da ma’aikatan zaɓen suka hallara, sai dai kuma gudanar da zaɓen ya gagara a rumfar inda a ƙarshe aka kwashe kayan zaɓe. Daya daga cikin ma’aikatan…
Read More
Gwamna El-Rufai ya shafe awanni a layi domin kaɗa ƙuri’arsa a Kaduna

Gwamna El-Rufai ya shafe awanni a layi domin kaɗa ƙuri’arsa a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shiga jerin gwano domin kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa ta PU024 da ke Unguwan Sarki a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 25 ga watan Febrairu yayin babban zaɓen shugaban ƙasa, El-Rufa'i ya koka da yadda talakawa suka ƙi fitowa kaɗa ƙuri'a a Kaduna, bayan da shafe sama da sa'o'i biyar akan layin kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa, inda ya bayyana damuwarsa kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar. Da yake jawabi…
Read More
Zaɓen Gwamnoni: Na yaba da aikin BVAS – Shugaban NITDA

Zaɓen Gwamnoni: Na yaba da aikin BVAS – Shugaban NITDA

Daga ABUBAKAR M. TAHIR Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi CCIE, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda zaɓen gwamnoni yake cigaba da gudana a faɗin ƙasar nan. Khashifu Inuwa ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da ya kaɗa ƙuriarsa a akwati mai lamba 004 dake 'Yan Dutsina, a mazaɓar Kasuwar Ƙofa dake Hadejia, Jihar Jigawa. Ya ce, "Haƙiƙa na yaba da aikin BVAS mai tantance masu zaɓe, inda cikin ƙasa da daƙiƙa talatin ta yi aikinta jami'an zaɓe suka tantance ni na karɓi katin zaɓena". Ya ƙara da cewa, kowa ya…
Read More