Siyasa

Zaɓen Gwamnoni: Gwamna Makinde ya kai bantensa

Zaɓen Gwamnoni: Gwamna Makinde ya kai bantensa

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ƙarƙashin Jam'iyyar PDP. Makinde ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 563,617 yayin da Sanata Teslim Folarin na APC ya rufa masa baya da ƙuri'u 251,230, sannan Adebayo Adelabu na jam'iyyar of the Accord ya zo na uku inda ya tsira da ƙuri'u 38,757. A ranar Asabar aka gudanar da zaɓen gwamna a jihohi 28 daga cikin 36 da ƙasar ke da su. Jihohi takwas ɗin da ba a yi zaɓen gwamna a cikinsu ba sun haɗa…
Read More
Ƙananan hukumomi 8 sun gabatar da sakamakon zaɓen gwamna a Sakkwato

Ƙananan hukumomi 8 sun gabatar da sakamakon zaɓen gwamna a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ya zuwa yanzu ƙananan hukumomi takwas daga cikin 23 ne suka gabatar da sakamakon zaɓukkansu. Ƙananan hukumomin sun haɗa da Binji wanda APC ta samu ƙuri'u dubu 13,410 yayin da PDP ke biye mata da ƙuri'u 11,078, sai kuma ƙaramar hukumar Wurno inda APC ke da ƙuri'u 17,350 sannan PDP na da 13,099. Sai kuma ƙaramar hukumar Yabo da jamiyyar APC ta samu ƙuri'u 14,729 inda PDP ta tashi da ƙuri'u 12,014. Haka lamarin yake a ƙaramar hukumar Isa, inda ɗan takarar APC, Ahmad Aliyu, ya doke abokin karawarsa Malam Saidu Umar da ƙuri'u 13,632,…
Read More
PDP ta ƙwace kujerar Kakakin Majalisar dDokokin Yobe da ta mahaifar shugaban Majisar Dattawa

PDP ta ƙwace kujerar Kakakin Majalisar dDokokin Yobe da ta mahaifar shugaban Majisar Dattawa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Sakamakon da hukumar zaɓe INEC ta sanar na zaɓen 'yan majalisar dokokin jihar Yobe, ya nuna ɗan takarar jam'iyyar PDP, Hon. Musa Lawan Majakura ya lallasa na jam'iyyar APC, wanda shi ne Kakakin majalisar, Hon. Ahmed Lawan Mirwa a mazaɓar Nguru ta waje. Sakamakon ya nuna jam'iyyar PDP ta samu ƙuri'u 6,648 yayin da APC ta samu ƙuri'u 6,466 a zaɓen, wanda hakan ya bai wa ɗan takarar PDP nasarar lashe zaɓen. Hon. Majakura na PDP ya lallasa Hon. Ahmed Mirwa ne bayan da ya kwashe shekaru 20 yana jan zarensa a kujerar, daga 2003…
Read More
Zaɓen Gwamnoni: APC ta lallasa PDP a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa

Zaɓen Gwamnoni: APC ta lallasa PDP a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu A ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen Gwamna da na 'yan majalisun dokoki, wanda malamar zaɓe a rumfa mai lamba 001 dake cikin Makaranar Firamaren Katuzu, a Gashuwa ta jihar Yobe ta jagoranta, Shugaban Majisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya lashe mazaɓarsa da tazara mai yawa a zaɓen. Da take bayyana sakamakon, jami'ar zaɓen, Malama Rahama Ahmad ta ce ɗan takarar Gwamna a jam'iyyar APC shi ne ya samu gagarumar nasara a rumfar zaɓen da yawan ƙuri'a 435 yayin da abokin takararsa na PDP ya samu ƙuri'a 295.
Read More
Jam’iyyar PDP ta lallasa APC a gidan gwamnatin Kaduna

Jam’iyyar PDP ta lallasa APC a gidan gwamnatin Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kaduna ta sha kaye a akwatunan zaɓe biyun da ke Gidan Sir Kashim Ibrahim, fadar gwamnatin jihar. Ɗan takarar gwamna na PDP, Alhaji Isa Ashiru Kudan ne ya lashe akwati mai lamba 014 da ƙuri’u 77 yayin da ɗan takarar APC, Sanata Uba Sani ya samu ƙuri’u 40. Jami’in zaɓe Mohammed Baso ya ce jam’iyyun PRP da NNPP sun samu ƙuri’u ɗai-ɗaya. Haka ma akwatu mai lamba 013 PDP ta yi nasara da ƙuri’u 69 yayinda APC ta samu 64. Jami’in zaɓe Kalu Kelechi Michael ya ce jam’iyyar LP ta samu…
Read More
INEC ta ɗage zaɓen gwamna zuwa Lahadi a rumfunan zaɓe 10 a Legas

INEC ta ɗage zaɓen gwamna zuwa Lahadi a rumfunan zaɓe 10 a Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ɗage zaɓen gwamna da na majalisar jiha a wasu rumfunan zaɓe guda 10 a yankin Lekki, Jihar Legas. Kwamishinan INEC na jihar, Segun Agbaje, shi ne ya sanar da haka ga manema labarai. A cewarsa, wasu masu yi wa ƙasa hidima da INEC ta ɗauka aikin wucin-gadi sun yi zargin an kama su yayin zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata yayin da suka yi yinƙurin shiga yankin. Ya ce bayan da ma'aikatansu suka shirya kayan aiki, mazauna yankin sun ji tsoron fitowa gudun kada ɓata-garin yankin su fafare su, su tarwatsa…
Read More
Ubangiji Ya riga ya zaɓi wanda zai zama Gwamnan Kano – Gawuna

Ubangiji Ya riga ya zaɓi wanda zai zama Gwamnan Kano – Gawuna

Daga RABI'U SANUSI a Kano. Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa Allah Ya riga ya zaɓi wanda zai zama gwamna a Jihar Kano tun fil azal. Gawuna ya bayyana haka ne yayin da yake kaɗa ƙuri'arsa da safiyar Asabar a mazaɓarsa dake Gidan Nasiru Ahli dake Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano. Ya ce yana da tabbacin samun nasara a wannan zaɓe wanda a cewarsa yana gudana cikin kwanciyar hankali. "Ba zan yi ƙasa a gwuiwa ba wajen cewa Ubangiji ke ba da mulki, mun kuma yi zaɓe kamar yadda mutane suka…
Read More
’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wuraren zaɓe a Legas

’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wuraren zaɓe a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mutum ɗaya ya rasa ransa, wasu da dama sun samu raunuka bayan da ’yan daba suka kai farmaki a rumufunan zaɓe a sassan Jihar Legas. An gano cewa an bindige mutum ɗaya har lahira, wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da ɓata-garin suka yi dirar mikiya a wuraren zaɓen. Yankunan da aka kai hare-haren sun haɗa da Ikota, Jakande, Ijegun, Festac da kuma Isolo. Rikicin ya fara ɓarkewa ne bayan ɓata-garin sun kutsa cikin yankin Okota, inda jam’iyyar LP ke da ƙarfi. Maharan sun fatattaki mutanen da suka fito yin kaɗa ƙuri'a, sannan suka…
Read More
Bayan shafe sa’o’i uku a kan layi, Gwamna El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa

Bayan shafe sa’o’i uku a kan layi, Gwamna El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bayan haƙuri a kan layi na tsawon lokaci, gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sauke nayinsa na jama'a a mazaɓarsa na PU024 da ke Unguwar Sarki GRA a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa. Da yake magana da manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa, El-Rufai ya ce, ana neman masu kaɗa ƙuri’a a yankin Kudancin Kaduna da su zaɓi wata jam’iyya ko kuma su koma gidajensu. Ya ce, a halin yanzu jami’an tsaro na gudanar da bincike a jihar. Gwamnan ya ce, an gudanar da zaɓen a wasu rumfunan zaɓe ba tare da wata matsala ba. “Babu komai,…
Read More