Siyasa

APC za ta gana da zaɓaɓɓun ‘yan majalisunta kan shugabancin Majalisar Tarayya

APC za ta gana da zaɓaɓɓun ‘yan majalisunta kan shugabancin Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar APC za ta gana da zaɓaɓɓun sanatoci da mambobin Majalisar Wakilai ya zuwa ranar Litinin mai zuwa domin tattauna batun shugabancin Majalisa karo na 10 da ake shirin kafawa. Kwamitin Gudanarwa na jam'iyyar ns Ƙasa ne zai gana da 'yan majalisun inda ake sa ran samar da tsare-tsaren da za su taimaka wa 'yan jam'iyyar samun muƙamai a shugabancin majalisun. Sanarwar taron wadda aka fitar ranar Juma'a da daddare, mai taken "Gayyata zuwa ga ɗaukacin zaɓaɓɓun sanatoci da 'yan Majalisar Wakilai”, Sakataren jam'iyyar na Ƙasa, Sanata Iyiola Omisore ne ya rattaba mata hannu. “Ana sanar da…
Read More
Wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin ƙaddamar da Majalisar Dokokin Ƙasar karo na 10 a watan Yuni, wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman shugabancin majalisar. Ana sa ran masu neman kujerun majalisar dattawa da ta wakilai za su fara bayyana sha’awarsu a kan muƙaman da suka zaɓa da zarar majalisar dokokin ƙasar ta dawo daga hutun zace a ranar 20 ga watan Maris. Baya ga shugabancin majalisar dattawa, sauran muqaman da za a naɗa sun haɗa da kakakin majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa da kuma manyan muƙamai. Bisa al'adar majalisa, manyan mambobi - 'yan majalisa masu wa'adi biyu…
Read More
Yuguda ya bayyana Tinubu a matsayin mai amana

Yuguda ya bayyana Tinubu a matsayin mai amana

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya bayyana dalilansa na goyon bayan shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya danganta da riƙon amanarsa, musamman tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari. "Kamar yadda muka sani, Allah ya yi ikonSa, Tinubu shi ne sanadi da ya sanya masoyinmu Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasar Nijeriya. Inda bai ba shi goyon baya ba, bani tsammani zai kasance shugaba, in bacin wata ƙaddara ta Ubangiji," inji Yuguda. Yuguda, wanda yake yi wa manema labarai jawabi a garin Bauchi, ya kuma bayyana cewar, "Tinubu ya riƙe mu da amana, dalili…
Read More
Zan bai wa ƙananan hukumomi ’yancin kansu idan na zama Gwamnan Kano, Cewar Gawuna

Zan bai wa ƙananan hukumomi ’yancin kansu idan na zama Gwamnan Kano, Cewar Gawuna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alƙawarin bai wa ƙananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Kano. Gawuna ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wani shiri na gidan talabijin ɗin NTA mai suna “The Balot”. Ya ce: “Ƙananan hukumomi wani ɓangare ne na gwamnati wanda ya fi kusa da jama’a wanda ke taimakawa wajen cigaban al’umma ta kowacce fuska," inji Gawuna. “A matsayina na tsohon shugaban ƙaramar hukumar na san abin da ya shafi…
Read More
Sanatan Kano ta Tsakiya: Kotu ta maye gurbin Shekarau da Rufai Hanga

Sanatan Kano ta Tsakiya: Kotu ta maye gurbin Shekarau da Rufai Hanga

Daga WAKILINMU Kotun Ƙoli ta maye sunan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau da na Rufai Hanga a matsayin zaɓaɓɓen Sanata na Kano ta Tsakiya karƙashin Jam'iyyar NNPP. Da yake yanke hukunci kan ƙarar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ɗaukaka kan hukuncin da Babbar Kotu mai zamanta a Abuja ta yanke da farko, Alƙalin Koton Ƙolin ya tabbatar da Hanga a matsayin ɗan takarar NNPP. Tun farko, Babbar Kotun Tarayya da Kotun Ɗaukaka Ƙara sun tabbatar da Rufai Hanga a matsayin Ɗan Takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam'iyyar NNPP biyo bayan janyewa da Ibrahim Shekarau ya yi…
Read More
Yadda aka tirsasa ni tafka maguɗin zaɓe don APC ta samu nasara – Farfesa Yakasai

Yadda aka tirsasa ni tafka maguɗin zaɓe don APC ta samu nasara – Farfesa Yakasai

Daga WAKILINMU Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana yadda aka tilasta masa tafka maguɗi a sakamakon zaɓe a matsayinsa na Baturen Zaɓe a yankin Tudun Wadah, Kano, yayin zaɓen da ya gudana. Cikin wasiƙar da ya aika wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Ibrahim Yakasai ya aibata sakamakon zaɓen da ya bayyana bayan kammala zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya. A cewarsa, tilasta masa aka yi kan ya tafka maguɗin zaɓe bayan da aka jefa rayuwarsa cikin haɗari a zahiri. Ya ce galibin sakamakon zaɓen da jami’an zaɓe suka bayyana ba na…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bai wa Tinubu damar bincikar kayayyakin zaɓe

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bai wa Tinubu damar bincikar kayayyakin zaɓe

Daga BASHIR ISAH Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPC) mai zamanta a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta bai wa Hukumar Zaɓe (INEC), umarnin ta bai wa zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado Bola Tinubu, damar bincikar muhimman kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanarda zaɓen Shugaban Ƙasa. Tinubu da Jam'iyyar APC sun buƙaci kotu ta ba su damar duba kayayyakin zaɓen ne domin tattara bayanan da za su yi amfani da su wajen kare kansu a kotu daga ƙara da aka shigar a kansu. 'Yan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar…
Read More
Sanatoci sun karɓi shaidar lashe zaɓensu

Sanatoci sun karɓi shaidar lashe zaɓensu

Daga BASHIR ISAH A ranar Talata Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga sanatocin da suka yi nasara a zaɓen da ya gabta. Shugaban INEC na ƙasa, Mahmood Yakubu, shi ne ya jagoranci miƙa shaidar ga sanatocin wanda ya gudana a Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja. A jawabin da ya yi ran Asabar da ta gabata, Yakubu ya ce 423 ne suka lashe kujerun majalisun tarayya, yayin da za a sake zaɓe a wasu mazaɓu 46. Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da sanatoci 98 daga cikin 109 da ake da…
Read More
INEC ta miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Wakilai shaidar lashe zaɓe

INEC ta miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Wakilai shaidar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga 'yan Majalisar Wakilai da suka lashe zaɓe a zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu. A ranar Laraba INEC ta miƙa wa 'yan majalisar shaidarsu a Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja. Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da sanatoci 98 daga cikin 109 da ake da su, sai kuma 'yan Majalisar Wakilai 325 daha cikin 360 da ake da su.
Read More
Masari ya karɓi jiga-jigan PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC

Masari ya karɓi jiga-jigan PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP tare da magoya bayansu 10,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Katsina. Akasarin waɗanda suka kwashe kayansu daga jam'iyyar ta PDP zuwa APC na hannun daman tsohon gwamnan jihar ne, wato Ibrahim Shehu Shema. Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya karɓe su a gidan gwamnatin jihar. Sauya sheƙar na zuwa ne 'yan kwanaki kaɗan kafin gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a ranar Asabar, 11 ga watan Maris. Daraktan yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina Ahmed Musa Ɗangiwa ne ya bayyana wa manema…
Read More