Siyasa

Sunan Alhassan Doguwa ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen waɗanda suka ci zaɓe

Sunan Alhassan Doguwa ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen waɗanda suka ci zaɓe

Daga BASHIR ISAH Sunan Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakila, Alhassan Ado Doguwa, ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen 'yan majalisun da suka lashe zaɓe a zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana ranar 25 ga Fabrairu. Wannan na zuwa ne bayan da kotu ta amince ta ba da belin ɗan majalisar wanda ke tsare a kurkuku bisa zargin haddasa rikicin siyasa. Duk da dai an ayya Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen yankinsu, sai dai ba a ga sunansa ba daga jerin sunayen 'yan takarar da Hukumar INEC ta fitar a ranar Talata…
Read More
Ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba ya ƙin sakamakon zaɓe ko da an tafaka maguɗi – Tinubu

Ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba ya ƙin sakamakon zaɓe ko da an tafaka maguɗi – Tinubu

Daga WAKILINMU Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba zai ƙi karɓar sakamakon zaɓe ba ko da kuwa an tafka maguɗi a zaɓen. Tinubu ya faɗi haka ne a matsayin martani ga 'yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi. Tun ana tsaka da tattara ƙurin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana, Atiku da Obi suka buƙaci a soke zaɓen. Sun bukaci hakan ne bayan da suka yi zargin an tafa maguɗi sakamakon rashin amfani da na'urar BVAS. Da yake amsa tambayar manema labarai bayan ziyarar…
Read More
Kotu ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a Zamfara

Kotu ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau. Kotun Ƙolin ta tabbatar da Dr. Dauda Lawal Dare a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar Gwamna ƙarƙashin Jamiyyar PDP a zaɓen da za a gudanar ranar Asabar Mai zuwa. Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu kafin zaɓen gwamnanoni da na 'yan majalisun jiha da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya a jihohi 36 na ƙasar nan. Kotun Ɗaukaka Ƙara reshen Sokoto ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a ranar 6 ga watan Janairun 2023 inda ta soke zaɓen fidda gwani…
Read More
Zaɓen gwamnoni: Kowa ya shiga tetayinsa, gargaɗin ‘yan sandan Kano ga masu shirin tada tarzoma

Zaɓen gwamnoni: Kowa ya shiga tetayinsa, gargaɗin ‘yan sandan Kano ga masu shirin tada tarzoma

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta gargaɗi duk wasu dake da niyyar haifar tashin hankali a zaɓen gwamnoni da majalisar jihar da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na rundunar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi. Jami'in ya ce dangane da bayanai da rundunar ke samu na ɗaura ɗamarar da wasu shugabanin siyasar suke yi na yunƙurin yin ta'ammali da 'yan dabar siyasa don tayar da tarzoma yayin zaɓe mai zuwa a jihar. Sanarwar ta ce, "kamar yadda…
Read More
Ba za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba – Ezeife

Ba za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba – Ezeife

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon gwamnan jihar Anambara, Chukwuemeka Ezeife, ya ce, ba za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya ba. Ezeife ya bayyana haka ne a yayin da ya ke zargin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da yin maguɗin zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya inda jam’iyyarAPC da ɗan takararta Bola Ahmed Tinubu suka marawa baya. Tsohon shugaban na Anambra ya ce, a fili yake cewa Peter Obi na jam'iyyar LP ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasar. Shugaban Hukumar INEC, Mahmood Yakubu,…
Read More
INEC ta tsayar da lokacin miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisun tarayya shaidar lashe zaɓe

INEC ta tsayar da lokacin miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisun tarayya shaidar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH Ya zuwa ranakun Talata da Laraba masu zuwa ake sa ran Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga 'yan majalisun tarayya da suka kai bantensu a zaɓen da ya gudana. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ranar Asabar da safe yayin taronsu da Kwamishinonin Zaɓe (REC) a Abuja. Yakubu ya ce 'yan majalisu 423 ne suka ci zaɓe, yayin da za a sake zaɓen 'yan majalisu a wasu mazaɓu 46. Ya ce, 'yan majalisun da suka ci zaɓen sun haɗa da sanatoci 98 cikin 109, da 'yan Majalisar Wakilai…
Read More
Jihohi 7 sun janye ƙarar da suka shigar kan nasarar Tinubu

Jihohi 7 sun janye ƙarar da suka shigar kan nasarar Tinubu

Daga BASHIR ISAH Bakwai daga cikin jihohi takwas da suka shigar da ƙara Kotun Ƙoli suna ƙalubalantar nasarar sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, sun janye ƙarar tasu. Sun janye ƙarar ne a ranar Juma'a, tare da miƙa wa kotun sanarwar janye ci gaba da shari'ar. Jihohin da lamarin ya shafa, da suka haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo, Taraba da kuma Sakkwato sun cimma wannan matsaya ne ta tawagar lauyoyinsu ƙarƙashin jagorancin Chief Mike Ozekhome (SAN). “Kotu ta sani cewa masu ƙara sun yanke janye ƙarar da suka shigar kan wanda ke kare kansa," in ji sanarwar.…
Read More
APC ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a Kebbi

APC ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  A cikin shirye-shiryenta na tinkarar zaɓen gwamnoni mai zuwa, Jam'iyyar APC mai mulki a Kebbi ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a jihar. Alhaji Isah Aslafi jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar ya bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja da cewa wannan ya biyo bayan ganin abinda ya faru ne a zaɓen da ya gabata na Shugaban Ƙasa da 'yan majalisun tarayya wanda 'mun lura da yadda zaɓen ya bar mu da mamaki, saboda muna ganin muna da nasara amma sai akasin haka ta faru." Ya ƙara da cewa duk da yake dai sun yaba da ƙoƙarin…
Read More
Bode George ya yi fatali da nasarar Tinubu, ya ce zai yi ritaya daga siyasa

Bode George ya yi fatali da nasarar Tinubu, ya ce zai yi ritaya daga siyasa

Daga BASHIR ISAH Tsohon gwamnan soji na Jihar Ondo, Bode George, ya bayyana zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisu da ya gudana ranar Asabar da ta gabata a matsayin abin kunya. George ya ce Shugaban INEC ya gaza, bayan da ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin zai gudanar da zaɓe.mai tsabta ta amfani da na’ura, amma a ƙarshe lamari ya sauya. Kazalika, ya ce zai yi ritaya daga harkokin siyasa bayan kammala zaɓen gwamnoni ranar 11 ga Maris. Bode George, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a shiyyar Kudu maso Yamma, ya bayyana nasarar da Ahmed Tinubu a…
Read More
Na rungumi ƙaddarar faɗuwa zaɓe, ba zan je kotu ba, inji Kabiru Gaya

Na rungumi ƙaddarar faɗuwa zaɓe, ba zan je kotu ba, inji Kabiru Gaya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa ya rungumi ƙaddarar faɗuwa zaɓen Majalisar Dattawa na shiyyar Kano ta Kudu da aka gudanar, wanda Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na Jam’iyyar NNPP ya yi nasara. Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon murya da aka raba wa manema labarai a Kano ranar Litinin. Kabiru Gaya ya kuma taya Kawu Sumaila murnar lashe zaɓen, tare da ba shi tabbacin ba zai ƙalubalanci sakamakon zaven a kotu ba. ”Sau huɗu na ci zaɓen Sanatan Kano ta Kudu, shekaru 16 kenan. Kuma a cikin…
Read More