03
Mar
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa ya rungumi ƙaddarar faɗuwa zaɓen Majalisar Dattawa na shiyyar Kano ta Kudu da aka gudanar, wanda Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na Jam’iyyar NNPP ya yi nasara. Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon murya da aka raba wa manema labarai a Kano ranar Litinin. Kabiru Gaya ya kuma taya Kawu Sumaila murnar lashe zaɓen, tare da ba shi tabbacin ba zai ƙalubalanci sakamakon zaven a kotu ba. ”Sau huɗu na ci zaɓen Sanatan Kano ta Kudu, shekaru 16 kenan. Kuma a cikin…
