Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jami’in tattara sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Ribas, Farfesa Teddy Charles Adias, ya dakatar da aikin tattara sakamakon zaɓe saboda abin da ya bayyana a matsayin barazana ga rayuwarsa.
Kafin dakatarwar, an tattara sakamakon ƙananan hukumomi 21 cikin 23 na jihar.
Sakamako ne kawai daga ƙananan hukumomin Obio Akpor da Degema, wanda aka ce za a tattara a safiyar yau.
Adias, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya, Otuoke, Jihar Bayelsa, ya sanya ranar Talata don tattara sakamako a ƙananan hukumomin.
Sai dai a safiyar ranar Talata, ya ce waɗanda ke yi wa rayuwarsa barazana sun zarge shi da alhakin duk wani maguɗin zaɓe da ake zarginsa da shi a Ribas.
Ya ce ya samu kira da dama daga waɗanda ba a san ko su waye ba bayan an nuna lambar wayarsa ta sirri a shafukan sada zumunta.
Farfesan ya sha alwashin ba zai cigaba da tattara sakamakon ba har sai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta magance lamarin.