Siyasa

Tinubu ya yi wa Atiku ƙafar baya a Zamfara

Tinubu ya yi wa Atiku ƙafar baya a Zamfara

Daga AMINU AMANAWA Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa babban abokin karawarsa Atiku Abubakar ƙafar baya a zaɓen shugaban ƙasa na jihar Zamfara. Baturen zaɓen jihar Zamfara Farfesa Kasim Shehu ya sanar da cewa Bola Tinibu na jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u dubu 298, 396 yayin da Atikun ke biye masa da ƙuri'u dubu 193, 978. Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ya samu ƙuri'u 4044 yayin da Peter Obi na Labour ke da yawan ƙuri'u dubu 1,660. Yayin sanarwar dai baturen ya ce hukumar ta soke zaɓen…
Read More
Zaɓen Sanatan Kebbi ta Arewa bai kammala na – INEC

Zaɓen Sanatan Kebbi ta Arewa bai kammala na – INEC

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Hukumar INEC ta ce za Kamar yadda bayanai suka zo daga hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta an bayyana za a sake zabe a rumfuna 30 masu ƙuri'u 16,940. Rumfanan zaɓen da lamarin ya shafa sun haɗa da: Arewa rumfa 1, mai lamba 02Argungu rumfa 2, mai lamba 03.Augie rumfa 4, mai lamba 04.Bagudo rumfa 4, mai lamba 05.Dandi rumfa 7, mai lamba 08.Suru rumfa 12, mai lamba 018. Tazarar da ɗan takarar Sanata na PDP, Dr. Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabin Argungu ya bai wa takwaransa na APC, Dr. Hussaini Suleiman…
Read More
Gwamna Bagudu ya sha kaye a hannun Aliero

Gwamna Bagudu ya sha kaye a hannun Aliero

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Hukamar zaɓe mai kanta ta Ƙasa reshen Jihar Kebbi ta ayyana Sanata Muhammad Adamu Aliero na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen takarar Sanatan Kebbi ta Tsakiya. Atiku Bagudu dai shi ne gwamnan jihar ta Kebbi kuma ɗan takarar kujerar majalisar dattawa a ƙarƙashin APC, ya sha kaye a hannun Sanata Aliero da rinjayen ƙuri'u sama da 35,000 bayan kammala tattara sakamakon zaɓen mazaɓar Gundumar Kebbi ta tsakiya.
Read More
Kwankwaso ya lallasa Tinubu da Atiku a Kano

Kwankwaso ya lallasa Tinubu da Atiku a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu 2023, Daga ƙarshe dai an kammala tattara sakamakon na ƙananan hukumomin 44 na jihar Kano. Don haka an ayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kano, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da ƙuri’u 479,938. Jihar Kano ta na da masu kaɗa ƙuri’a kusan 5,792,848 wadanda aka yiwa rijista, ya yinda aka tantance masu kaɗa ƙuri’u…
Read More
Atiku ya lashe Sakkwato

Atiku ya lashe Sakkwato

*Mutum 254,902 ba su samu damar jefa ƙuri'a ba - INEC Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, yayi nasarar doke abokan fafatawarsa a Sokoto. Atiku ya samu nasarar ne da ƙuri'u 288,679 wanda hakan ya ba shi damar doke babban abokin karawarsa na APC, Bola Ahmed Tinubu da ya samu ƙuri'u dubu 285,444. Tunda farko, Tinubu ne ke kan gaba, amma daga bisani lamarin ya bayan isowar sakamakon ƙaramar hukumar Tambuwal da ya ba wa Atiku nasarar da tazarar ƙuri'u 3,235. Peter Obi na Labour party ne ya zama n 3 a jihar…
Read More
Atiku ya lashe mazaɓu 9 daga cikin 10 a Kebbi ta Tsakiya

Atiku ya lashe mazaɓu 9 daga cikin 10 a Kebbi ta Tsakiya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe ƙananan hukumomi 9 cikin 10 da aka kammala ƙirgawa inda ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar, APC Bola Ahmed Tinubu, ya lashe ƙaramar hukuma ɗaya. An kusa kammala kidayar kuri'un dan takarar Sanata na Kebbi ta tsakiya. Yanzu haka an tattara sakamakon ƙuri'u na ƙananan hukumomin Gwandu, Aliero, Kalgo, Bunza, Koko Besse, Maiyama, da Jega. Sai dai har yanzu ana jiran sakamakon ƙaramar hukumar Birnin kebbi. Rahotanni na cewa an sami hakan ne sakamakon batan dabon Jami'in tattara sakamakon zaɓe na gundumar Marafa…
Read More
Obasanjo ya buƙaci a soke sakamakon zaɓe a wuraren da na’uran BVAS ta samu matsala

Obasanjo ya buƙaci a soke sakamakon zaɓe a wuraren da na’uran BVAS ta samu matsala

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Yakubu Mahmood, da ya bayyana soke sakamakon zaɓe a rumfunan da hukumar zaɓen ta samu matsalar aiki da na'urar BVAS a zaɓen ranar Asabar da ta gabata. Zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya. Obasanjo a wata wasiƙa da ya fitar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar Litinin, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya kauce wa abin da ya kira hatsarin da ke kunno kai na ba da umarnin…
Read More
Zaben Sanatan Yobe ta Kudu bai kammalu ba – INEC

Zaben Sanatan Yobe ta Kudu bai kammalu ba – INEC

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Hukumar INEC ta ayyana zaɓen kujerar Sanatan Yobe ta Kudu a matsayin wanda bai kammala ba. Babban jami'i mai kula da zaɓen shiyyar, Farfesa Shettima Abdulkadir Saidu, shi ne ya sanar da hakan da yammacin yammacin Litinin a garin Potiskum. A cewar Baturen zaben, matakin ya zo ne sakamakon wasu matsalolin da suka jawo rusa zab'ɓen rumfar zabe mai lamba 003 a Gundumar Manawaci, dake ƙaramar hukumar Fika, inda adadin ƙuri'un da aka jefa a rumfar suka zarta waɗanda aka tantance a zaɓen.
Read More
Ɗan Yariman Bakura ya lashe kujerar Majalisar Tarayya a mazaɓun Maradun/Bakura a zamfara

Ɗan Yariman Bakura ya lashe kujerar Majalisar Tarayya a mazaɓun Maradun/Bakura a zamfara

Daga RABIU SANUSI Bayanai daga Jihar Zamfara na bayyana cewa ɗan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma sanatan ɗaya daga shiyyoyin jihar, Ahmad Sani Muhammad Yariman Bakura, ya lashe zaɓen kujerar Majalisar Tarayya ƙarƙashin mazaɓun Bakura da Maradun. Hon Ahmad Sani Muhammad Bakura ya samu wannan nasarar ne da ƙuri'a 55,273 inda ya doke abokin takarar sa Muhammad Bakura Ahmed wanda ya samu kimanin ƙuri'a 17,559 Sakamakon Wanda baturen zaɓe na mazaɓar, wato Dr. Ahmad Kainuwa na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau ya bayyana a hedikwatar tattara sakamakon zaben dake Maradun. Ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC…
Read More
Tinubu ya doke Atiku a Ogun

Tinubu ya doke Atiku a Ogun

Daga AISHA ASAS An bayyana ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin zakaran zaɓen da aka gudanar ranar Asabar na Jihar Ogun, inda ya kayar da abokin karawarsa, ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu. Kamar yadda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a Ogun ta sanar, ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar APP, Bola Tinubu ya yi nasarar lashe zaɓen jihar ne da ƙuri'u 341,554, yayin da ɗan takara a Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zo na biyu da ƙuri'u 123,831. Sauran jam'iyyun da suka biyo bayan su sun…
Read More