Zaben Sanatan Yobe ta Kudu bai kammalu ba – INEC

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Hukumar INEC ta ayyana zaɓen kujerar Sanatan Yobe ta Kudu a matsayin wanda bai kammala ba.

Babban jami’i mai kula da zaɓen shiyyar, Farfesa Shettima Abdulkadir Saidu, shi ne ya sanar da hakan da yammacin yammacin Litinin a garin Potiskum.

A cewar Baturen zaben, matakin ya zo ne sakamakon wasu matsalolin da suka jawo rusa zab’ɓen rumfar zabe mai lamba 003 a Gundumar Manawaci, dake ƙaramar hukumar Fika, inda adadin ƙuri’un da aka jefa a rumfar suka zarta waɗanda aka tantance a zaɓen.