Gwamna Bagudu ya sha kaye a hannun Aliero

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Hukamar zaɓe mai kanta ta Ƙasa reshen Jihar Kebbi ta ayyana Sanata Muhammad Adamu Aliero na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen takarar Sanatan Kebbi ta Tsakiya.

Atiku Bagudu dai shi ne gwamnan jihar ta Kebbi kuma ɗan takarar kujerar majalisar dattawa a ƙarƙashin APC, ya sha kaye a hannun Sanata Aliero da rinjayen ƙuri’u sama da 35,000 bayan kammala tattara sakamakon zaɓen mazaɓar Gundumar Kebbi ta tsakiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *