Tinubu ya doke Atiku a Ogun

Daga AISHA ASAS

An bayyana ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin zakaran zaɓen da aka gudanar ranar Asabar na Jihar Ogun, inda ya kayar da abokin karawarsa, ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu.

Kamar yadda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a Ogun ta sanar, ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APP, Bola Tinubu ya yi nasarar lashe zaɓen jihar ne da ƙuri’u 341,554, yayin da ɗan takara a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zo na biyu da ƙuri’u 123,831.

Sauran jam’iyyun da suka biyo bayan su sun haɗa da Jam’iyyar LP, mai ƙuri’u 85,829, sai Jam’iyyar ADC a matsayin ta uku da ƙuri’u 10,529. Ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya samu ƙuri’u 2,200.

Adadin waɗanda suka yi rajistar zaven ya kai 2,687,606, yayin da waɗanda aka tantance suka kai 612,341. Adadin ƙuri’u masu inganci da aka kaɗa su ne 611,448, yayin da aka watsar da ƙuri’u 31,324.