Oshiomhole ya lashe kujerar Sanatan Edo ta Arewa

Daga AISHA ASAS

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta tabbatar da Adams Oshiomhole na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar Asabar na kujerar Sanatan Edo ta Arewa.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen ranar Lahadi a Auchi, jami’in zaɓen Farfesa Benjamin Adesina, ya bayyana Oshiomhole a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 107,110 waɗanda suka ba shi damar kayar da sanata mai ci, sanata Francis Alimekhena, na Jam’iyyar PDP, mai ƙuri’u 55,344.

“Adams Oshiomhole na Jam’iyyar APC ne ya samu ƙuri’u mafi rinjaye, don haka ya lashe zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, na kujerar Sanatan Edo ta Arewa,” inji Adesina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *