27
Feb
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya sha kaye a yunƙurinsa na neman kujerar ɗan majalisar dattawan na mazaɓar Arewa maso Yamma a jihar Benuwai a hannun tsohon mai taimaka masa, Titus Zam na jam’iyyar APC. Jami’in bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Rufus Shaato, ya bayyana Zam a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazaɓar Benuwai na Arewa maao Yamma a ofishin INEC da ke Makurdi. Shaato ya ce, Zam ya samu ƙuri'u 143,151 da ya lashe zaɓen yayin da Ortom ya samu ƙuri'u 106,882 ya zo na biyu yayin da ɗan takarar jam'iyyar LP, Mark Gbillah ya…
