Siyasa

NNPP ta buga ɗan gidan Ganduje da ƙasa, ta lashe zaɓen ɗan majalisa a Kano

NNPP ta buga ɗan gidan Ganduje da ƙasa, ta lashe zaɓen ɗan majalisa a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Abba Abdullahi Umar Ganduje, ɗa a gurin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya faɗi zaɓen ɗan majalisar wakilai a Kano. Ɗan gidan gwamnan wanda ya fito takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓun Tofa da Rimingado, ya sha ƙasa bayan da abokin karawarsa Tijjani Abudlkadir Jove, ɗan takarar jam'iyyar NNPP ya buga ahi da ƙasa. Jove wanda shi ne wakilin riƙon ƙwarya na wakilcin majalisar, zai maimaita kujerar tasa ne a karo na biyar. An kaɗa wa Jove ƙuri'u 52, 456 yayin da Abba Ganduje shi kuma ya samu ƙuri'u 44,809.
Read More
Ƙanen tshohon Shugaban Ƙasa ‘Yar’adua ya lashe zaɓen sanatan Katsina ta Tsakiya

Ƙanen tshohon Shugaban Ƙasa ‘Yar’adua ya lashe zaɓen sanatan Katsina ta Tsakiya

Daga UMAR GARBA a Katsina Abdul'azizi Musa Yar'adua, ƙane ga tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua, ya samu nasarar lashe zaɓen ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Katsina ta tsakiya Babban jami'in dake bayyana sakamako farfesa Aminu Ɗalhatu Kankia ne ya sanar da hakan inda ya bayyana cewar 'Yar'adua ya samu ƙuri'a 153,512. Inda ya doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Aminu Surajo Makera wanda ya samu ƙuri'a 152,140. Sai kuma ɗan takarar jam'iyyar NNPP Gambo Abubakar Jally ke mara masu baya da ƙuri'a 1,605 sai kuma Muhammad Mustapha Kurfi na jam'iyyar SDP ya samu ƙuri'a 807 a…
Read More
Al-Makura ya sha kaye a zaɓen Sanatan Nasarawa ta Kudu

Al-Makura ya sha kaye a zaɓen Sanatan Nasarawa ta Kudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma Sanata Umaru Tanko Al-Makura, mai wakiltan Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa ƙarƙashin Jam'iyyar APC, ya sha kaye a zaɓensa na sake tsayawa takara a hannun Mohammed Ogishi-Onawo na Jam’iyyar PDP. Da yake bayyana sakamakon zaɓen a ranar Litinin a Lafiya, babban birnin jihar, Farfesa Ahmed Ashiku, jami’in zaɓen, ya bayyana cewa Ogoshi Onawo ya samu ƙuri’u 93,064 inda ya doke Sanata mai ci Al-Makura wanda ya samu ƙuri’u 76,813. Ashiku, yayin da yake bayyana cewa Onawo, bayan ya cika sharuɗɗan doka kuma ya samu mafi yawan ƙuri'u, an…
Read More
Jami’in tattara sakamakon zaɓen Sanatan Kebbi ta Tsakiya ya yi ɓatan-dabo

Jami’in tattara sakamakon zaɓen Sanatan Kebbi ta Tsakiya ya yi ɓatan-dabo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da harhaɗa sakamakon zaɓen Sanatan Kebbi ta Tsakiya sakamakon ɓacewar jami’in da ke wakiltar mazaɓar Marafa, a Birnin Kebbi. An buƙaci ya koma gefe ya daidaita wasu bambance-bambance a cikin alƙaluman sakamakon da ya kawo wa cibiyar tattara bayanan lokacin da ya ɓace kuma ba a iya gano shi ba tun ranar Lahadi. Jami'in tattara sakamakon zaɓen, ya yi ɓatan-dabo ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Lahadin da ta gabata. Sakamakon da ake magana a kai na tsakanin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da…
Read More
Gwamna Sani Bello ya lashe kujerar Sanatan Neja ta Arewa

Gwamna Sani Bello ya lashe kujerar Sanatan Neja ta Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja ya lashe zaɓen kujerar Sanatan Neja ta Arewa a ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar APC. Bello ya samu ƙuri’u 12,044 inda ya doke ɗan takarar Jam’iyyar PDP da ya zo na biyu. Da yake bayyana sakamakon zaɓen a Kontagora, jami’in zaɓen Farfesa Kolo Zacchaeus, ya ce Bello ya samu ƙuri’u 100,197 inda ya kayar da ɗan takarar PDP, Shehu Muhammad Abdullahi wanda ya samu ƙuri’u 88,153 da na New Nigeria Peoples Party, Ibrahim Wali, wanda ya samu ƙuri'u 13,886.
Read More
Minitar Kuɗi da na Noma sun sha kaye a rumfar zaɓensu a Kaduna

Minitar Kuɗi da na Noma sun sha kaye a rumfar zaɓensu a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed da takwaranta a ma’aikatar noma, Mahmud Muhammad Abubakar sun sha kaye a rumfunan zaɓensu a hannun ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar. Ministocin ‘yan asalin Jihar Kaduna ne kuma a halin yanzu suna cikin Majalisar Ministocin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Ministar Kuɗi, Hajiya Zainab Ahmed ta sha kashi a rumfar zaɓenta mai lamba 053 a Kawo, Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, inda a zaɓen Shugaban Ƙasa APC ta samu ƙuri’u 8, NNPP 5, Jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 15. Ministan Noma, Mahmud Muhammad Abubakar ya sha…
Read More
SDP ta lashe zaɓen Sanata a shiyyar Shugaban APC na Ƙasa a Nasarawa

SDP ta lashe zaɓen Sanata a shiyyar Shugaban APC na Ƙasa a Nasarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Ahmed Wadada na Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin wanda ya lashe zaven mazaɓar Nasarawa ta Yamma. Mataimakin Farfesa Nasirudeen Baba, jami’in zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC a mazabar Nasarawa ta Yamma ne ya bayyana hakan bayan kammala tattara sakamakon zaɓen a ranar Litinin a cibiyar tattara sakamakon zaɓe na shiyya da ke ƙaramar hukumar Keffi a jihar. Ya bayyana cewa bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, Wadada ya samu ƙuri’u 96,488 yayin da ɗan takarar Jam’iyyar…
Read More
Atiku ya yi nasara a Yobe

Atiku ya yi nasara a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa a jihar Yobe. Sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 17 wanda Hukumar zaɓen ta kammala tattarawa da daren ranar Lahadi, ya nuna Atiku ya lashe zaɓen da yawan ƙuri'u 198,567, inda abokin fafatawarsa, Tinubu ya samu ƙuri'u 151,459. Da yake sanar da sakamakon zaɓen, Baturen zaɓen Shugaban Ƙasa a jihar Yobe, kuma Shugaban Jami'ar Tarayya dake Kashere, a jihar Gombe, Farfesa Umaru Pate, ya bayyana jam'iyyar NNPP, ta Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wadda ta zo ta uku…
Read More
PDP ta lashe kujerar Majalisar Wakilai a mazaɓar Fune/Fika a Yobe

PDP ta lashe kujerar Majalisar Wakilai a mazaɓar Fune/Fika a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Ɗan takarar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, Engr. Mohammed Buba Jajere, ya lashe zaɓen Majalisar Wakilai a mazaɓar Fune/Fika da ke jihar Yobe. Da yake sanar da sakamakon zaɓen a garin Damagum, shalkwatar ƙaramar hukumar Fune, Baturen zaɓen, Farfesa Johnson Sunday Alao, ya ayyana jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta samu ƙuri'u 32,464. Ya ce APC ta samu ƙuri'u 31,969, NNPP 1011, ADC 400, YPP 125, SDP 108 da jam'iyyar AA mai ƙuri'u 78.
Read More
Sanata Akwashiki ya kai bantensa a Nasarawa

Sanata Akwashiki ya kai bantensa a Nasarawa

Daga WAKILINMU Hukumar zaɓe, INEC, ta ayyana Sanata Godiya Akwashiki na jam'iyyar SDP a matsayin wanda ya lashe kujerar sanata a Nasarawa ta Arewa a zaɓen da ya gudanar ranar Asabar. Baturen zaɓe, Farfesa Ilemona Adofu na Jami'ar Tarayya da Lafia, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen ranar Litinin a Akwanga. Ya ce Akwashiki lashe zaɓen ne da ƙuri'u 44,47, inda abokin hamayyarsa na APC, Alhaji Danladi Halilu Envuluanza ya samu ƙuri'u 32,058.
Read More