Atiku ya yi nasara a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa a jihar Yobe.

Sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 17 wanda Hukumar zaɓen ta kammala tattarawa da daren ranar Lahadi, ya nuna Atiku ya lashe zaɓen da yawan ƙuri’u 198,567, inda abokin fafatawarsa, Tinubu ya samu ƙuri’u 151,459.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen, Baturen zaɓen Shugaban Ƙasa a jihar Yobe, kuma Shugaban Jami’ar Tarayya dake Kashere, a jihar Gombe, Farfesa Umaru Pate, ya bayyana jam’iyyar NNPP, ta Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wadda ta zo ta uku a zaben da ƙuri’u 18,270.