SDP ta lashe zaɓen Sanata a shiyyar Shugaban APC na Ƙasa a Nasarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Ahmed Wadada na Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin wanda ya lashe zaven mazaɓar Nasarawa ta Yamma.

Mataimakin Farfesa Nasirudeen Baba, jami’in zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC a mazabar Nasarawa ta Yamma ne ya bayyana hakan bayan kammala tattara sakamakon zaɓen a ranar Litinin a cibiyar tattara sakamakon zaɓe na shiyya da ke ƙaramar hukumar Keffi a jihar.

Ya bayyana cewa bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, Wadada ya samu ƙuri’u 96,488 yayin da ɗan takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Shehu Tukur ya samu ƙuri’u 47,717.

Ya ci gaba da cewa Mista Musa Galadima na Jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 46,820.

Sai dai ya ƙara da cewa jimillar ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen sun kai 234,040, yayin da jimillar ƙuri’u 228917 da aka ki amincewa da su 5123.

Kalamansa: “Ni Mataimakin Farfesa Nasirudeen Baba a nan na tabbatar da cewa ni ne jami’in tattara sakamakon zaɓen takarar Sanatan Nasarawa ta Yamma a zaɓen 2023 da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

“Wannan Wadada Ahmed na SDP bayan ya cika sharuɗɗan doka an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma an dawo da shi.”

Yakubu Mohammed-Salisu, wakilin SDP na zaɓen, ya danganta nasarar da Wadada ta samu ne ga magabatansa na wayar da kan matasa da talakawa da kuma samun zuciyar al’ummar yankin Sanatan Nasarawa ta Yamma saboda kyautatawa da yake yi musu.

“Wannan zaɓen zavin mutane ne,” inji shi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Gundumar Nasarawa ta Yamma ce Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya fito kuma shi ne Sanata mai wakiltar shiyyar a Majalisar Dattawa kafin a zave shi a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa a 2022.