Gwamna Sani Bello ya lashe kujerar Sanatan Neja ta Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja ya lashe zaɓen kujerar Sanatan Neja ta Arewa a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC.

Bello ya samu ƙuri’u 12,044 inda ya doke ɗan takarar Jam’iyyar PDP da ya zo na biyu.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen a Kontagora, jami’in zaɓen Farfesa Kolo Zacchaeus, ya ce Bello ya samu ƙuri’u 100,197 inda ya kayar da ɗan takarar PDP, Shehu Muhammad Abdullahi wanda ya samu ƙuri’u 88,153 da na New Nigeria Peoples Party, Ibrahim Wali, wanda ya samu ƙuri’u 13,886.