Sanata Akwashiki ya kai bantensa a Nasarawa

Daga WAKILINMU

Hukumar zaɓe, INEC, ta ayyana Sanata Godiya Akwashiki na jam’iyyar SDP a matsayin wanda ya lashe kujerar sanata a Nasarawa ta Arewa a zaɓen da ya gudanar ranar Asabar.

Baturen zaɓe, Farfesa Ilemona Adofu na Jami’ar Tarayya da Lafia, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen ranar Litinin a Akwanga.

Ya ce Akwashiki lashe zaɓen ne da ƙuri’u 44,47, inda abokin hamayyarsa na APC, Alhaji Danladi Halilu Envuluanza ya samu ƙuri’u 32,058.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *