Siyasa

Ɗan takarar PDP ya doke ƙanin Abdulsalami Abubakar a Neja

Ɗan takarar PDP ya doke ƙanin Abdulsalami Abubakar a Neja

Daga WAKILINMU Ɗan takarar Majalisar Wakilai na PDP a shiyyar Chanchaga a jihar Neja, Abubakar Abdul Buba, ya doke takwaransa na APC Abubakar Adamu wanda ƙani ne ga tsohon Shugaban Ƙasa Janar Abdulsalami Abubakar. Da take bayyana sakamakon zaɓe a Minna babban jihar, baturiyar zaɓen, Farfesa Mercy Modupe Adeyeye, ta ce Buba (PDP) ya samu ƙuri'u 35,688, yayin Ado Salami (APC) ya tsira da ƙuri'u 19, 282. Ta ce ɗan takarar NNPP, Ibrahim Abdulaziz, ya samu ƙuri'u 1,747, sannan ɗan takarar APGA, Usman Musa Ndakpayi, ya samu 2,548, yayin da Abdullahi Musa na jam'iyyar Labour ta ƙare da ƙuri'u 2,…
Read More
Tinubu ya doke Atiku a Kwara

Tinubu ya doke Atiku a Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar Asabar a ƙananan hukumomi 16 na Jihar Kwara. Tinubu ya samu ƙuri’u 263,572 inda ya kayar da abokin hamayyarsa kuma ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 136,909. Adadin waɗanda suka yi rajistar zaven ya kai 1,695,928 yayin da waxianda aka tantance suka kasance 497,519. Jimillar quri'u masu inganci da aka kaɗa 469,971; Waɗanda aka watsar 26,712 sai jimillar ƙuri'un sa aka…
Read More
Atiku ya cinye Katsina

Atiku ya cinye Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi wa sauran abokan hamayyarsa zarra inda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa bayan da aka sanar da sakamakon zaɓen da aka tattara daga ƙananan hukumomi 34 dake jihar. Jami'in zaɓen Farfesa Mu'azu Gusau ne ya sanar da hakan a ɗakin da ake tattara sakamakon zaɓen Farfesa Gusau ya bayyana cewar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri'a 489,045 a yayin da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ya samu ƙuri'a 482,283, sai Rabi'u Musa Kwankwaso ya samu ƙuri'a 69,385 sai kuma Peter Obi…
Read More
Gwamna Ayade ya sha kaye a hannun Jarigbe a takarar Sanatan Kuros Ribas

Gwamna Ayade ya sha kaye a hannun Jarigbe a takarar Sanatan Kuros Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kuros Ribas a majalisar wakilai ta ƙasa, Sanata Jarigbe Agom Jarigbe na Jam’iyyar PDP, ya kayar da Gwamna Ben Ayade, inda ya lashe kujerar majalisar dattawa. Sanata Jarigbe ya samu ƙuri'u 76,145 inda ya doke Gwamna Ben Ayade wanda ya samu ƙuri'u 56,595. Da yake bayyana Sanata Jarigbe a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanata da sanyin safiyar ranar Litinin, 27 ga wata, 2023, jami’in zaɓen, Dokta Emmanuel Emanghe wanda ya yi magana a madadin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ya yaba wa masu ruwa da…
Read More
Sanata Lawan ya lashe mazaɓarsa a Yobe ta Arewa

Sanata Lawan ya lashe mazaɓarsa a Yobe ta Arewa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya lashe mazaɓarsa ta Arewacin Yobe da gagarumar nasara a zaɓen majalisun tarayya da na Shugaban ƙasa wanda ya gudana ranar Asabar a faɗin kasar. Da take sanar da sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Lahadi, Baturiyar zaɓen (Returning Officer), Farfesa Omolola Aduloju, daga Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashu'a, a cibiyar tattarawa da sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi shida na Yobe ta Arewa, Bade, Jakusko, Karasuwa, Nguru, Yusufari da Machina, ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda ya samu…
Read More
Goje ya lashe kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya

Goje ya lashe kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Ɗanjuma Goje na Nam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Gombe ta Tsakiya. Jami’in zaɓe na INEC Farfesa Mustapha Muhammad wanda ya bayyana sakamakon zaɓen a ranar Lahadi a Kumo, ya ce Goje ya samu ƙuri’u 102,916. Ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Aliyu Abubakar na Jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 37,870, da Mista Bibikir Muhammad na Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), wanda ya samu ƙuri’u 1,155. Goje shi ne ɗan majalisar dattawa mai wakiltar mazaɓar majalisar dattijai kuma ya…
Read More
INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen Shugaban Nijeriya zuwa Litinin

INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen Shugaban Nijeriya zuwa Litinin

Daga SANI AHMAD GIWA Shugaban Hukumar Zaven Nijeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ɗage zaman tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar zuwa ranar Litinin. Farfesa Mahmood ya bayyana hakan ne bayan gabatar da sakamakon jihar Ekiti a zauren tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar. Shugaban na INEC ya ce kasancewar jihar Ekitin ce kaɗai ta kai sakamakonta zuwa zauren tattara sakamakon zuwa yanzu, hukumar ta ɗage karvar sakamakon zuwa ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Read More
Datti Baba-Ahmed ya sha kaye a hannun Atiku a akwatin sa

Datti Baba-Ahmed ya sha kaye a hannun Atiku a akwatin sa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party, LP, ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP. A rumfar zace mai lamba 021 dake Unguwar Tudun Wada, a Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, adadin waɗanda aka tantance sun kai 272. Jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 102, inda ta lashe rumfunan zaɓe, sai kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ƙuri’u 98. Jam'iyyar LP ta zo ta uku da ƙuri'u 54, yayin da NNPP ta samu ƙuri'u 11.
Read More
PDP za ta yi na’am da sakamakon zaɓe – Tambuwal

PDP za ta yi na’am da sakamakon zaɓe – Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Babban mai yekuwar neman zaɓen Atiku Abubakar kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ce Jam'iyyar PDP za ta karɓi sakamakon zaɓe hannu bibbiyu duk yadda ya kasance. Tambuwal ya bayyana hakan ne a mahaifarsa, Tambuwal, jim kaɗa bayan kaɗa ƙuri'arsa. “Mun sani cewa duk yadda lamari ya samu ɗan Adam daga Ubangiji ne, haka shi ma shugabanci Ubangiji kan bayar da shi ga wanda ya so a kuma duk lokacin da Ya so". A cewarsa, "ganin yadda alumma suka fito zaɓe, wata manuniya ce da ke nuni da yadda jama'a suka bai wa sha'nin…
Read More