Datti Baba-Ahmed ya sha kaye a hannun Atiku a akwatin sa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party, LP, ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.

A rumfar zace mai lamba 021 dake Unguwar Tudun Wada, a Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, adadin waɗanda aka tantance sun kai 272.

Jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 102, inda ta lashe rumfunan zaɓe, sai kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ƙuri’u 98.

Jam’iyyar LP ta zo ta uku da ƙuri’u 54, yayin da NNPP ta samu ƙuri’u 11.