Kwankwaso ya lashe zaɓe a ƙaramar hukumar Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Dan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya lashe zaɓe a Ƙaramar Hukumar Dakin Tofa inda Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya fito.

A sakamakon da jami’in INEC na Ƙaramar Hukumar, Adamu Jibril Alhassan ya sanar a hukumar zaɓe ta jihar Kano, ya ce NNPP ta samu ƙuri’a 16,773, yayin da NNPP ta samu 25,072.

Kazalika, ya ce PDP ta samu ƙuri’a 2,477 sai kuma jam’iyyar LP da ta tsira da ƙuri’u 202.