PDP za ta yi na’am da sakamakon zaɓe – Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Babban mai yekuwar neman zaɓen Atiku Abubakar kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ce Jam’iyyar PDP za ta karɓi sakamakon zaɓe hannu bibbiyu duk yadda ya kasance.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a mahaifarsa, Tambuwal, jim kaɗa bayan kaɗa ƙuri’arsa.

“Mun sani cewa duk yadda lamari ya samu ɗan Adam daga Ubangiji ne, haka shi ma shugabanci Ubangiji kan bayar da shi ga wanda ya so a kuma duk lokacin da Ya so”.

A cewarsa, “ganin yadda alumma suka fito zaɓe, wata manuniya ce da ke nuni da yadda jama’a suka bai wa sha’nin zaɓe muhimmanci wanda da ma hakan shi ne babban ƙudurin jam’iyyarmu ta PDP,” inji shi.

Don haka ya yi kira ga alumma da su kasance masu bin doka da oda yayin da ake sanar da sakamakon zaɓe.