Gwamna Ayade ya sha kaye a hannun Jarigbe a takarar Sanatan Kuros Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kuros Ribas a majalisar wakilai ta ƙasa, Sanata Jarigbe Agom Jarigbe na Jam’iyyar PDP, ya kayar da Gwamna Ben Ayade, inda ya lashe kujerar majalisar dattawa.

Sanata Jarigbe ya samu ƙuri’u 76,145 inda ya doke Gwamna Ben Ayade wanda ya samu ƙuri’u 56,595.

Da yake bayyana Sanata Jarigbe a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanata da sanyin safiyar ranar Litinin, 27 ga wata, 2023, jami’in zaɓen, Dokta Emmanuel Emanghe wanda ya yi magana a madadin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ya yaba wa masu ruwa da tsaki kan yadda suka gudanar da zaɓen cikin lumana.

Emanghe ya kuma yaba wa dukkan jami’an tsaro da suka bada gudunmuwa wajen tabbatar da tsaro wanda ya kai ga samun nasara da ingantaccen zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *