Atiku ya cinye Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi wa sauran abokan hamayyarsa zarra inda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa bayan da aka sanar da sakamakon zaɓen da aka tattara daga ƙananan hukumomi 34 dake jihar.

Jami’in zaɓen Farfesa Mu’azu Gusau ne ya sanar da hakan a ɗakin da ake tattara sakamakon zaɓen

Farfesa Gusau ya bayyana cewar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’a 489,045 a yayin da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 482,283, sai Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu ƙuri’a 69,385 sai kuma Peter Obi na jam’iyyar LP shi ya samu ƙuri’u 6,376.