26
Feb
Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewar, yana da yaƙin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar su ta PDP, Atiku Abubakar zai lashe kujerar shugabancin Najeriya. Inji gwamna, "A yanzu dai ba zance komai ba, amma muna jaddada tsammani ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, Wazirin Adamawa zai ci zaɓen nan da ikon Allah, da kuma sauran 'yan takarkari na sanatoci da 'yan majalisar tarayya. Sanata Bala Mohammed wanda yayi wannan furuci a mazabar sa ta Bakin Dutse dake garin Yelwan Duguri ta jihar Bauchi, ya kuma nuna gamsuwar sa da yadda na'urar…
