Zaɓen 2023: Abinda ya sa na kaɗa wa Tinubu ƙuri’a a filin Allah – Buhari

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilinsa na kaɗa wa Asiwaju TInubu ɗan takarar shugaban ƙasa a jamiyyar APC ƙuri’a a bainan nasi a yayin da yake zaɓe a mahaifarsa wato Daura.

Shugaban ya bayyana cewa, ba wani abu ne ya sa ya bayyana zaɓinsa ga Tinubun ba illa nuna biyayyarsa da goyon bayansa gare shi.

A cewar sa, bayan ya kewaye lungu da saƙo na ƙasar nan don yin yaƙin neman zaɓe ga tsohon gwamnan na Legas, ya kamata ya cika aikinsa na jaddada goyon baya a gare shi a matsayin wanda ya fi so ya gaji kujerarsa bayan ya sauka, ta hanyar kaɗa masa ƙuri’a.

Shugaban ya bayyana cewa, da ma shi mai goyon bayan takarar Tinubu ne a koyaushe, sannan ya nuna takardar zaɓensa ga manema labarai da kuma al’umma don su shaida irin jajircewarsa da goyon bayansa ga jam’iyyar APC da shugabancinta na ƙasa.

Buhari, wanda ya kaɗa ƙuri’arsa tare da matarsa Hajiya Aisha Buhari, da sauran iyalansa a rumfar zaɓe ta 003 a mazaɓar A ta yankin Sarkin Yara a Daura, ya bayyana cewa, abin takaici ne matuƙa a ce ‘yar takarar gwamna guda ɗaya ce tak mace ta tsaya a APC, wato Aisha Binani, inda ya nemi da a goya wa ‘yar takarar baya.

Sannan ya bayyana jin daɗinsa na yadda mutane suka fito suka yi tururuwa wajen zuwa yin zaɓe.

“Na ji daɗi matuƙa saboda na ga mutane da dama sun fito. Na ji daɗi sosai kuma ina murna.

“Shi kuma ɗan takarar da na zaɓa, na riga na ambace shi a jihohi da dama a jihohin Nasarawa, Katsina da Sokoto.

“Ko ina na ambaci mafi soyuwar ɗan takarata wato Asiwaju Tinubu, kuma na san ‘yan mazabata za su yi shi ɗari bisa ɗari”. Inji shi.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabbatar da an kare musu haƙƙinsu na zaɓe, duk wani ɗan takarar da suke son su zaɓa, an bar su sun yi shi.

Da yake amsa tambayar ko yaya ya ji a karo na farko tun bayan zaɓen shekarar 2023 ba ya cikin takardar zaɓe?

Shugaban ya bayyana cewa, abin nishaɗi ne hakan sosai. “…Na kalli waɗanda suke takara da juna wasu daga cikinsu duk sun bi sun rikice, ba su san cewa ni sai da na gwada sau uku kuma na dangana da kotun ƙoli shi ma har sau uku”.

“A karo na 4 na ce, akwai Allah ai, sai Allah Ya aiko da wata fasaha, da katin zaɓe na dindindin, saboda haka ba wani mazambacin mutumin da ya isa ya ƙwace komai”. A cewar sa.

A cewar sa kuma, APC ce za ta lashe zaɓe tun daga Daura har zuwa Legas.

Bayan shugaban ya kaɗa ƙuri’arsa, su ma iyalan gidansa suka kaɗa nasu ƙuri’unsu a nan.