Siyasa

Har yanzu ban janye wa wani ba, inji ɗan takarar gwamnan Nasarawa a NNPP

Har yanzu ban janye wa wani ba, inji ɗan takarar gwamnan Nasarawa a NNPP

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a inuwar Jam’iyyar NNPP, Alhaji Yakubu Maidoya ya ƙaryata jita-jitar da wasu a jihar ke yaɗawa a yanzu cewa ya janye wa gwamnan jihar wanda shine kuma ɗan takarar Jam’iyyar APC mai ci a jihar, Injiniya Abdullahi Sule. Alhaji Yakubu Maidoya ya sanar da haka ne a jawabinsa a lokacin wata tattaunawar haɗin gwiwa da jam’iyyarsa ta NNPP da ‘yan takarar gwamnan a inuwar jam’iyyun SDP da ADC wadda suka gudanar da manema labarai a babbar sakatariyar ‘yan jarida dake Lafiya, babban birnin jihar ranar Laraba 15 ga…
Read More
Zaɓen gwamnoni: A ina za a iya yin ‘inconclusive’ bana?

Zaɓen gwamnoni: A ina za a iya yin ‘inconclusive’ bana?

*Ba a san maci tuwa ba..! Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gobe ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki na jihohi a Tarayyar Nijeriya, waɗanda ake sa ran rantsarwa a ranar 29 ga Mayu, 2023, bayan kammala wa’adin zangon gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na jihohi. Zaɓen da ya gabata na 2019 ya zo da wani sabon salon ƙa’idar da ba a saba gani ba a zaɓukan baya, inda ba a sanar da sakamakon zaɓe bisa dalilin wata kalma ta ‘inconclusive’, wacce ta ke nufin ‘rashin kammaluwa’ ko kuma ‘zaɓen da bai kammalu ba’. Shin mene ne…
Read More
Bincike: Babu abin da za ku nema ku rasa, cewar INEC ga jam’iyyar LP

Bincike: Babu abin da za ku nema ku rasa, cewar INEC ga jam’iyyar LP

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce a shirye take ta ba da damar bincikar bayanan zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu ga duk jam'iyyar da ke da buƙatar hakan. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar lauyoyin Jam'iyyar Labour ƙarƙashin jagorancin Dr Livy Uzoukwu, SAN, ranar Litinin a Abuja. Da yake jawabi, Yakubu ya faɗa wa lauyoyin cewa ya samu sanarwar zuwansu ta wasiƙar da aka aiko masa mai ɗauke da kwanan wata 6 ga Maris, don bincikar kayayyakin da aka yi amfani da su…
Read More
Ba ni da zaɓin wani wanda nake so ya zama Kakaki ko Shugaban Majalisa – Tinubu

Ba ni da zaɓin wani wanda nake so ya zama Kakaki ko Shugaban Majalisa – Tinubu

Daga AMINA YUSUF ALI Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa, sam shi ba shi da wani wanda ya fi so ya zama shugaban majalisun dokoki guda biyu da ake sa ran za su kafa majalisa a karo na 10 a Nijeriya. Tinubu, wanda zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da sababbin zaɓaɓɓun 'yan majalisun. Majiyarmu ta bayyana cewa, a yanzu dai, Tinubu ya ce har yanzu ba shi da wani wanda ya zaɓa da yake son ya shugabanci majalisun guda biyu, wato shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin…
Read More
Shugaban APC ya amince akwai aibi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar

Shugaban APC ya amince akwai aibi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Litinin ya ce, zaɓen shugaban ƙasa da ’yan majalisun tarayya wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 ba cikakken mara naƙasu bane, domin an samu aibi. Adamu ya faɗi haka ne a yayin da yake jawabi a wurin taron kwamitin gudanarwa na APC da shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima da zaɓaɓɓun mambobin majalisar tarayya. Taron na sirri wanda bai fara gudana ba sai da misalin ƙarfe 2:48 na rana a ɗakin taro na Banquet House da ke Abuja. Daga…
Read More
Kar a zargi Gwamna Buni wajen faɗuwar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa a Yobe – Injiniya Umar Ali

Kar a zargi Gwamna Buni wajen faɗuwar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa a Yobe – Injiniya Umar Ali

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu An bayyana cewa rashin wakilci nagari, ta fuskar 'yan majalisar dokokin Yobe, shugabanin ƙananan hukumomi, tare da wakilan al'umma a matakai daban-daban a matsayin tarnaƙin da ya dabaibaye jam'iyyar APC ta sha mummunan kaye, a zaɓen Shugaban Ƙasa haɗe da na 'yan majalisun a makonnin da suka gabata a jihar Yobe. Wannan furucin ya fito ne daga bakin ɗan takarar Gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin jam'iyyar APC da NNPP a zaɓukan fidda-gwani na shekarar 2019 da 2022, Engr. Malam Umar Ali, wanda halin yanzu na hannun daman Gwamnan jihar Yobe ne, Mai Mala Buni, a…
Read More
NNPP ta kori ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar da wasu ƙusoshinta a Katsina

NNPP ta kori ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar da wasu ƙusoshinta a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Jam'iyyar NNPP a Jihar Katsina ta kori wasu jiga-jigan jam'iyyar ciki har da mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar, Muttaqa Rabe Darma da shugaban jam'iyyar, Alhaji Sani Liti da sakatarenta Alhaji Mustapha Bashir da kuma shugaban matasa da shugabannin jam'iyyar na shiyyoyin Katsina, Daura da kuma Funtua. Kakakin jam'iyyar, Alhaji Nasiru Usman Kankia ne ya bayyana wa manema labarai hakan lokacin da yake ƙarin bayani dangane da lamarin a Katsina. A cewar kakakin, an kori mutanen ne bisa aikata laifin yi wa jam'iyya zagon ƙasa. Ya ƙara da cewa shugabannin jam'iyyar sun kira wani taron da…
Read More
Me ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya?

Me ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ai duk masu sharhi na magana kan abin da ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya na 2023 inda hakan ya kawo lokacin da shugaban da ke kan gado Muhammadu Buhari ke shirin ajiye mulki ranar 29 ga watan mayu don ƙarewar wa’adin mulkin saka gabaɗaya bisa tandain tsarin mulki. Bayan kammala zaɓen da aka haqqaqe ya fi kowanne raba kan ’yan Nijeriya ta fuskar bambancin addini da ƙabilanci har ma da vangaranci, hakan wani darasi da kowane mai hankali ya kamata ya zauna shi kaɗai ya yi nazarin makomar Nijeriya kafin ma a je ga makomar…
Read More
Ban ce a zaɓi wani ɗan takara ba baya ga Abba Gida-gida – in ji Kawu Sumaila

Ban ce a zaɓi wani ɗan takara ba baya ga Abba Gida-gida – in ji Kawu Sumaila

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Zaɓaɓɓen sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewar ba gaskiya ba ne jita-jitar da ke yawo cewar yana mara wa wata jam'iyya baya a zaɓen gwamna da ke tafe. Mataimaki na musamman ga Sanata Sumaila a kan yaɗa labarai, Abbas Adam Abbas, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Asabar a Kano Abbas ya ce, wannan labari ba shi da tushe balle makama. Ya bayyana cewa wasu masu neman tayar da zaune tsaye gami da yarfen siyasa ne ke yaɗa wannan labari na…
Read More
Ba a yi zaɓen Shugaban Nijeriya kan tsarin INEC ba – Chatham House

Ba a yi zaɓen Shugaban Nijeriya kan tsarin INEC ba – Chatham House

Daga AMINA YUSUF ALI Chatham House, wata ƙungiya ce mai zaman kanta a kan dokoki wacce take a Landan, ta bayyana cewa, daga nazarin da ta yi na zaɓen shugaban ƙasa ya bayyan cewa har yanzu hukumar zaɓe ta INEC ba ta koyi sababbin darasi ba. Ƙungiyar wacce Dakta Leena Koni Hoffmann, ta yi rubutun jawabin nan a maimakonta, ta ƙara da cewa, hukumar zaɓen ta kasa bin tsarinta wanda ta tsara da kanta kafin zaɓen, musamman ma da ta ce za ta dinga ɗora sakamakon zaɓe kai-tsaye.  Ƙungiyar mai zamanta a Landan ta yi misali da alƙalumman Fitch Solutions…
Read More