Cire ni daga sarautar Kano ba zai hana ni cigaba da faɗin gaskiya ba – Khalifa Sanusi II

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Kano Murabus Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa duk da an cire shi daga sarauta, zai ci gaba da bayyana gaskiya da faɗin ra’ayinsa wajen kare ƙasa da sake gina Nijeriya.

Muhammadu Sanusi wanda shi ne Khalifan Tijjnaniya na Nijeriya, ya bayyana haka a Abuja yayin da ya ke magana a wurin da aka yi wata diramar dave, mai nuna bayanin cire shi daga sarauta zuwa lokacin naɗa shi Khalifan Tijjnaniya.

Diramar mai suna “Emir Sanusi: Truth in Time”, an nuna ta ne a babban ɗakin taro na ‘Yar’Adua Centre, Abuja a ranar Asabar.

Farfesan tsara wasan dirama, Ahmed Yarima na Jami’ar Redeemer ne ya rubuta diramar, yayin da Joseph Edgar na kamfanin shirya finafinai na Duke of Somolu Productions ne furudusan wasan.

Sanusi ya ce yana da ƙwarewar da zai iya bayarwa wajen gina ƙasar nan, idan ya yi la’akari da daɗewar da ya yi yana yi wa ƙasar nan aiki.

Ya ce ya yi aiki a Bankin UBA, First Bank da kuma zama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), kuma ya yi Sarkin Kano tsawon shekaru shida, yanzu ga shi Khalifan Tijjnaniya.

Ya ce idan har ya nuna fushi da da-na-sani kan cire shi, to ya yi wa Allah rashin godiya kenan, idan ya yi la’akari da irin muƙaman da ya tava riƙewa.

“Ba na jin Allah ya ɗauke wata alfarmar da ya yi min don an cire ni kan mulki. Saboda haka ba ni da wani da-na-sani.”

Furudusan diramar mai suna Edgar, ya bayyana cewa an kashe Naira miliyan 40 wajen shirya diramar, wadda ya ce kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane 35 ne su ka ɗauki nauyin rabin kuɗin da aka kashe wajen shirya diramar.