Sarkin Musulmi ya jagoranci gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a Nijeriya

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kana Shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a Nijeriya, Alh Muhammad Sa’ad Abubakar III ya jagoranci gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya kan matsalar tsaro da ta addabi sassan Arewa da ma ƙasa baki ɗaya.

A wajen taron gudanar da addu’o’in da aka gudanar a masalacin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, babban limamin masallacin Juma’a na Sarkin Musulmi Muhammad Maccixo, Dr. Muhammad Sani Ɗangwaggo ya gabatar da ƙasida mai taken: ‘Muhimmancin Zaman Lafiya da Hanyoyin Tabbatar da Shi.

Manyan malamai ne dai dake a Sakkwaton da suka haɗar da Sarkin Malaman Sakkwato, Limamin Masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello da limamin masallacin Shehu da sauran limamai da malamai ne suka jagoranci gudanar da addu’o’in.

Ɗimbin al’ummar musulmi ne daga ƙungiyoyin addinin Musulunci daban-daban suka samu halartar taron, wanda aka yi makamancin shi a watan da ya gabata a masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello da ke daf da fadar mai Martaba Sarkin Musulmi a cikin garin Sakkwato.