PADWO ta karrama Sanata Yahaya a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ƙungiyar nan mai rajin taimaka wa marasa lafiya musamman marasa galihu (Patients and Destitute Welfare Organization (PADWO), da ke garin Argungu ta karrama Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa, tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa.

Da ya ke jawabi a madadin Sanata Dokta Yahaya Abubakar, babban hadiminsa Alhaji Bilyaminu Bawale Sardaunan Matasan Kabi, ya yaba wa wannan ƙungiyar bisa ga zaƙulo mutanen da ke taka muhimmiyar rawa wajen bayar da gudunmawar cigaban al’umma, wanda ba shakka zai zaburar da waɗansu don su ma su bayar da nasu gudummawar.

Haka zalika ya yaba wa wannan ƙungiyar bisa ga irin ayyukan da ta ke aiwatarwa ga marasa lafiya musamman marasa galihu da ke neman agaji.

Ya kuma bayar da tabbacin cigaba da bayar da gudummawar ta kowane vangare a duk lokacin da buƙatar ta taso kamar yadda ya saba, sannan kuma ana sa gudunmawa wajen gina makaratar koyon kiwon lafiya ya ci alwashin gina (Administrative block) a kan kuɗi Naira milliyan ɗari da saba’in domin amfanin al’umma.

Haka-zalika ya yi kira ga shugabanni musamman zaɓaɓɓu da su yi ƙoƙari su sauke nauyin da ke wuyansu na bayar da wakilcin da al’ummar su suka tura su saboda ko ba komai zai ba su natsuwa da samun sauƙi a ranar kiyama.

Tun farko da ya ke jawabi, Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya bayyana cewa wannan ƙungiyar ta yi tunani wajen zaƙulo mutanen da suka cancanci karramawa saboda ya zama zaburar da waɗansu masu hannu da shuni ko suka samu wata dama.

Ya yi kira ga waɗanda ke da hannu da shuni da kuma waɗanda ke riƙe da muƙaman da suke iya taimakawa al’umma musamman marasa galihu da su ƙara ƙaimi wajen saka jari a irin waɗannan ayyukan na taimakawa gajiyayyu da marasa ƙarfi.

Farfesa Mahmud Muhammed Garba shugaban ƙungiyar PADWO ya bayyana cewa dalilan da suka sanya karrama waɗannan mutane ashirin da shida sun haɗa da irin gudummawar da suke bai wa wannan ƙungiyar wajen tallafawa marasa lafiya da gajiyayyu.

Ya ƙara da cewa wannan ƙungiyar a koda yaushe ƙofarta buɗe ta ke wajen karvar tallafi saboda yawan samun mabuƙata da ta ke yi wanda a ƙiyasce tun kafa wannan ƙungiyar ta kashe sama da Naira milliyan ɗari musamman a ɓangaren marasa lafiya saboda a nan ne ta fi bai wa fifiko.