Akwai alamun ba gudu ba ja da baya a kan batun Taiwan

Daga LAWAL SALE

Hausawa dai na cewa: “komai nisan jifa, kasa za ta dawo”. A nan ina ma nuni da batun Taiwan a kan cewa ko ba daɗe, ko ba jima, Taiwan za ta dunƙule ko kuma za ta haɗe da jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, kasancewar Taiwan wani yanki ne ƙarƙashin ƙasar ta Sin.

A kwanan nan ne ofishin kula da harkokin Taiwan da na watsa labarai na majalisar gudanarwa ta ƙasar Sin a Beijing suka fitar da wata takardar bayani ƙaƙƙarfa mai taken “batun Taiwan da dunƙulewar ƙasar Sin a sabon zamani”.

Takardar dai tana ƙunshe da gargaɗi da jan kunne ga tsirarrun ’yan aware na tsibirin Taiwan tare da masu ingiza su daga ƙasashen ƙetare musamman ma ƙasar Amurka.

Idan ba a manta ba a wani ƙoƙarin tada zaune tsaye da Amurka ta yi a kwanan baya a yayin da kakakin majalisar wakilan ƙasar Nancy Pelosi ta kai ziyara tsibirin Taiwan duk da gargaɗin da ƙasar Sin ta yi, ya kawo cece kuce da gurbata dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

A sakamakon wannan tada husuma ne ma sojojin ’yantar da jama’ar ƙasar Sin (PLA) suka yi wani abun da ya nuna taunar tsakuwa domin aya ta ji tsoro a yankin tsibirin na Taiwan da kewaye domin miƙa saƙo cewa ƙasar Sin fa ba za ta yarda da wata rashin kunya da cin mutunci a yankin da ke mallakarta ba.

Kamar yadda na saba ambatar matsayina a kan batun Taiwan, ina nanata rashin gamsuwata ga yadda wasu ƙasashen ketare musamman Amurka take tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin, har ma a ce a kan batun Taiwan wanda ita kanta ƙasar Amurka ta tabbatar da yankin na Taiwan yanki ne na ƙasar Sin, kuma kasar Sin daya ce tak a duniya.

Ƙasar Amurkan dai ta rattaba hannu a shekarar 1978 a kan wannan batu.

Bugu da ƙari, akwai wani ƙuduri mai lamba 2758 wanda aka zartas a babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) da ya tanadi manufar ƙasar Sin daya ce a duniya, wanda ɗaukacin ƙasashen duniya sun yi ammana da shi.

Ina mai matuƙar jinjina ma ƙasar Sin da ta bugi gaba ta wallafa wannan takardar bayanin da ta nuna cewa ita fa ba kanwar lasa ba ce, kuma tana nan a kan bakanta na ganin cewa Taiwan ta dawo ta dunƙule da mahaifarta a tafarkin “kasa daya, tsarin mulki biyu”.

Kamar yadda na ambata da farko, sanin kowa ne cewa tun asali Taiwan yanki ne a ƙarƙashin ƙasar Sin kuma mallakarta ne, wannan batu dai yana da ingantaccen tushe na tarihi da doka.

A wasu bayanai da takardar da aka watsa suka ƙunsa, sun nuna cewa manufar ƙasar Sin daya tak, na wakiltar duk matsayar ƙasa da ƙasa, kuma ta yi daidai da ka’idojin huldar ƙasa da ƙasa.

A ƙarshe ina son jawo hankalin tsirarrun ’yan aware na Taiwan da ƙasashe masu zuga su da su yi hattara kuma su lura da take taken su wanda suke nuna neman tashin hankali ƙarara a tsibirin na Taiwan.

Jama’ar Taiwan kamar yadda tarihi ya nuna Sinawa ne, ba ja in ja a nan ya kamata su yi la’akari da cewa babu wanda zai fi son su idan ba ’yan uwansu Sinawa ba, kuma abun da ya fi masu alheri shi ne dunƙulewa da haɗewa da ainihin jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin domin ci gaba da samun zaman lafiya.

Babban kuskure ne idan Taiwan da ’yan awarenta suka ci gaba da bayar da kansu ga ’yan ƙasar waje masu neman fitina. Wannan ba abin da zai tsinana masu sai rikicin da ba wanda ya san yanda zai kare.