’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta sake kafa tarihi a wasan guje-guje

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta yi nasarar kare kambunta na gasar tseren mita 100 na ƙasashe renon Ingila, wato Commonwealth, bayan da ta kai matakin farko a ranar Lahadi a filin wasa na Alexander da ke Birmingham.

’Yar wasan ta sake kafa sabon tarihi bayan da ta kammala tseren mita 100 cikin daƙiƙa 20 da sakan 30, wanda hakan ya ba ta damar lashe lambar zinare ga ƙasarta Nijeriya.

Mai riƙe da kambun gasar ta duniya ta kawo ƙarshen tarihin tseren daƙiƙa 16 da sakan 65 da Brigitte Foster-Hylton ta Jamaica ta kafa a Melbourne, da ke ƙasar Australia.

Devynne Charlton daga Bahamas ce ta zo na biyu yayin da ’yar Birtaniya, Cindy Sember wacce ta yi bikin cikarta shekaru 28 ranar da samu nasara a wasan daf da na kusa da ƙarshe ta samu tagulla.