Ziyarar da Pelosi ta kai Taiwan tamkar zagon ƙasa ne ga dimukuraɗiyya

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya musanta kalaman kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi game da yankin Taiwan, a taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Jumma’a, inda ya nuna cewa matakin da Pelosi ta dauka na zuwa Taiwan, ba shi da wata alaka da dimokuraɗiyya, illa dai tauye tsarin dimokuradiyya, kuma hakan ya nuna yadda Amurka ta dora son kai sama da adalci na ƙasa da ƙasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, da wasu ‘yan majalisar da suka halarci ziyarar yankin Asiya, sun gudanar da taron manema labarai a kwanan baya. Pelosi ta ce, wannan ziyara ta shafi dimokuraɗiyyar Taiwan, wadda ta dace da manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tilo ta gwamnatin Amurka, kuma ba ta neman sauya yanayin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan.

Game da haka, Wang Wenbin ya ce, kalaman Pelosi sun kara tabbatar da cewa, ziyarar da ta kai yankin Taiwan na ƙasar Sin, goyon baya ne da suka yi ga masu neman ɓalle Taiwan daga ƙasar Sin.

Ƙasar Sin na da cikakken haƙƙi, kuma ya zama wajibi ta ɗauki ƙwararan matakan mayar da martani kan tsokanar Amurka, bisa la’akari da kare mulkin kai da cikakken yankin ƙasa, da kiyaye ƙa’idar dangantakar ƙasa da ƙasa, ta rashin tsoma baƙin cikin harkokin gida, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.

Mai fassara: Bilkisu Xin