Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta buƙaci zama da Shugaba Buhari a kan tsaron jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta fusata akan matsalar rashin tsaro dake cigaba da ƙara ƙamari a ƙauyuka da ƙananan hukumomin jihar wadda yanzu ta game har da babban birnin jihar.

Ɗaya daga cikin ‘yan majalisar Abubakar Muhammad Total wanda ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Funtuwa ya bayyana cewar matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka ba su da wani amfani illa ƙara takura al’ummar jihar saboda a cewarsa matakan ba su hana ‘yan ta’adda ci gaba da kai hare-hare ba.

Ya bada misali da dokar katse layukan sadarwa a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar.

“A ƙasa da shekara 1 gwamnati ta ɗauki matakai 5 a tunananin mu za a samu sauƙi an katse layin sadarwa kamata ya yi da aka katse layukan a nemi ‘yan ta’adda a hallaka su,” inji shi.

Ya cigaba da cewa katse layukan bai yi wani amfani ba saboda ‘yan bindigar ba su daina kai hari ba.

Ya kuma bayyana cewar sake dawo da dokar hana hawa babura daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 6 na safiya dokar bata da amfani illa ƙara wa al’umar jihar wahalhalu, inda ya ce dokar ba ta yi tasiri akan ‘yan ta’addar ba saboda su na cigaba da kai hare-hare akan babura.

Ya kuma ce hana sayar da man fetur a kasuwar bayan fage shi ma bai yi tasiri ba ga ‘yan ta’adda don kuwa su na amfani da babura a duk lolacin da za su kai hari.

Ya kuma soki matakin gwamnatin na hana aikin ‘yan sa kai, inda ya bayyana cewar gwamnati ta soke ‘yan sa kai amma kuma ba ta kawo madadinsu ba bayan an yi imanin ‘yan bindigar su na matuƙar tsoron ‘yan sa kai.

Mustapha Yusuf Jibiya ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Jibiya ya bayyana cewar majalisar za ta gana da Gwamna Masari da kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan matsalar rashin tsaron jihar a cewarsa idan Shugaba Buhari bai san tsananin matsalar rashin tsaro a jihar ba ko kuwa idan akwai wasu masu katange Shugaba Buhari daga sanin matsalar jihar majalisar ta yanke shawarar tunkarar shi gwa da gwa don tattauna matsalar rashin tsaron jihar da shi.

Majalisar dai ta fusata ne bayan da ta tafka muhawara akan wani ƙuduri da wasu ‘yan majalisar su ka gabatar a zauren majalisar kan matsalar rashin tsaro da ta wuce ƙauyuka da ƙananan hukumomin jihar ta shigo cikin babban birnin jihar.

Daga nan sai ya buƙaci majalisar da ta umarci gwamnatin jihar akan ta ta ɗauki ‘yan sa kai tare da horar da su ta kuma ba su bindigogi don tsaron jihar.

Daga ƙarshe shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Ali Abu Albaba ya nuna ɓacin ransa akan yawaitar matsalolin tsaro a Katsina, yana mai cewa Majalisar Jihar Katsina ta damu matuƙa akan yadda matsalar tsaro ta zama abun tsoro.

Albaba ya ce a duk rana sai majalisar ta karɓi labari kan hare haren ‘yan bindiga, wanda hakan ba ƙaramin abin tashin hankali ba ne da damuwa.

Ɗan majalisar ya bayyana cewar dole ne a magance wannan matsalar tsaro da ta addabi jihar yana mai cewa ba za su taɓa zura ido irin wannan lamari ya cigaba da faruwa.