‘Yan bindiga sun sace amarya da ango tare da kashe mutum biyu a garin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane ɗauke da bindigogi sun sake yin dirar mikiya a cikin birnin Katsina a wata unguwa mai suna Shola Quarters dake maƙotaka da asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya dake jihar Katsina.

Wani Mazaunin unguwar ya shaida wa Manhaja cewa ‘yan ta’addar sun shigo unguwar ne da misalin ƙarfe 1 da rabi na ranar Lahadi wayewar garin Litinin.

Ya ci gaba da cewa ‘yan ta’addar sun afka gidan wasu sababbin amare bayan da suka fasa gidansu ta baya inda su ka sace amaryar da angonta su ka kuma gudu da su ‘yan ta’addar waɗanda su ka shafe kusan sa’a ɗaya suna aikin ta’addanci sun kuma kashe wasu ‘yan banga a yayin da suka raunata wasu suka kuma arce da wasu mutanen zuwa daji.

‘Yan bangar sun gamu da ƙaddararsu ne bayan da suka yi ƙoƙarin hana ‘yan bindigar guduwa da amaren da suka sata.

Hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukansu a yayin da wasu ke kwance asibiti suna karɓar magani sakamakon raunin harbin bindiga.

Harin na zuwa ne kusan wata 2 bayan da Manhaja ta kawo labarin yadda ‘yan bindigar suka kai hari a unguwar ta Shola Quarters inda suka yi awon gaba da mutane da dama.

‘Yan bindigar sun addabi unguwar ta Shola Quarters sakamakon kusancin ta da dabar ɓarayin dajin dake ɓoye a dajukan dake cikin ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Jibiya, ɗaya daga cikin qananan hukumomin da matsalar tsaro ta fi shafa a jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce rundunar ta duƙufa don ganin ta ceto waɗanda aka yi garkuwar da su.

A wani labari mai kama da wannan, Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ya bayyana wa manema labarai cewa rundunar ta kuɓutar da wasu mutane shida da ɓarayi su ka yi garkuwa da su a ƙauyen Tandama na ƙaramar hukumar Ɗanja bayan wani samame da suka kai maɓoyar ‘yan ta’addar.

Haka zalika ya kuma ce sun yi nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan fashin daji Abdulkarim Faca-Faca da mutanensa bakwai a ƙarshen mako, bayan da wani wani jirgin yaƙi ya saki wuta akan maɓoyarsu.