Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da Ministan Abuja da Ministan Sufuri

Daga CMG HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya Cui Jianchun, ya gana da Ministan Abuja Muhammadu Bello da sabon Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, inda suka tattauna game da haɗin gwiwar ƙasashen biyu.


Taron wanda ya gudana a jiya, ya kuma samu halartar shugaban kamfanin CCECC mai ayyukan gine gine, dake ziyara a ƙasar, Liu Weimin.

Yayin ganawa tsakankin Cui Jianchun da Muhammadu Bello, sun waiwayi ci gaban da ɓangarorin biyu suka samu na haɗin kai a yankin hedkwatar ƙasar da ayyukan da suka ciyar da haɓakar tattalin arziki da samar da ilmi. Kuma ɓangarorin biyu sun kai ga matsaya cewa, za su ƙara haɗin kai a nan gaba, don fidda sabbin hanyoyin zuba jari da haɗin gwiwa da ma ingiza aikin shuka laimar kwaɗo na ba da misali.

Ban da wannan kuma, yayin da Cui Jianchun ya gana da Mu’azu Jaji Sambo, sun waiwayi haɗin gwiwar ɓangarorin biyu a fannin layin dogo, kan sun kai ga matsaya daya cewa, Najeriya mai faɗin filaye na da boyayyen karfi a fannin tattalin arziki, kuma ɓangarorin biyu za su duƙufa kan aikin kyautata yanayin tsarin layukan dogo a faɗin ƙasar, musamman ma layin dake tsakanin Kaduda da Katsina, inda za a yi ƙoƙarin ganin an fara amfani da shi a rabin farkon shekarar baɗi.

Fassarawar Amina Xu