‘Yan bindiga sun harbe babban jami’in Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu’ ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe babban jami’in Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS), Mohammed Kudu a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Lafiagi ta Jihar Kwara.

Jaridar This Day ta ruwaito babban jami’in watsa labarai na shugaban hukumar, Johannes Wojuola yana tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Kudu, wanda shi ne babban jami’in hukumar da ke kula da jihohin Kebbi, Sakkwato da Zamfara, ‘yan bindiga sun kashe shi ne ranar Lahadi.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS), tana baƙin cikin sanar da rasuwar Muhammad Kudu, sakamakon harbin da ‘yan bindiga suka yi masa a tsakanin Saminaka da Lambata, a lokacin da yake hanyar kowawa Kaduna daga Lafiagi ta Jihar Kwara ranar Lahadi.

Muhammad Kudu ya fara aiki da Hukumar FIRS ne a shekara ta 1993. Kafin rasuwarsa shi ne babban jami’in hukumar da ke kula da Kebbi, Sakkwato da Zamfara. Shi ne mataimakin Darakta wanda ya kwashe sama shekara 20 yana aiki tuƙuru ba ƙaƙƙautawa.”

Sanarwar ta isar da ta’aziyyar hukumar ga iyali da ‘yan’uwa mamacin, tare da ƙara ba su haƙuri a kan wannan mumman halin da suka samu kansu a ciki.

Marigayin ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya, kuma tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Lafiagi da ke Jihar Kwara ranar Litinin.

A yayin harin ‘yan bindigar sun kai hari wani gidan abinci mallakin Zainab Usman a garin Saminaka da ke Ƙaramar Hukumar Lapai a Jihar Neja, sun sace da wasu mata uku da ke mata aiki.

Maharan sun shiga garin ne da dare suka fara harbin kan mai uwa da wabi, wani daga cikin harsashe da suka harba ya samu wata tankar dakon man fetur, abin da ya sa gobara ta tashi, kamar yadda Abiodun Wasiu, kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ya tabbatar.