NDLEA ta cafke wani fasto da ke safarar ƙwayoyi a gangunan coci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), sun kama wani mai fataucin miyagun ƙwayoyi, Fasto Anietie Okon Effiong da ganguna uku na ‘crystal methamphetamine,’ wanda ake kira Mkpuru Mmiri, wanda ake kyautata zaton an shigo da su ne daga ƙasar Indiya.

Ƙwayoyin, waɗanda nauyinsu sun kai kilogiram 90, kuma aka loda su a cikin wata motar kasuwanci mai lamba RSH 691XC a Ojuelegba, Legas, an kama su ne a yayin da ake gudanar da bincike a kan babban titin Umuahia-Ikot Ekpene da ke Legas a ranar Asabar 6 ga watan Agusta 2022, inda aka saka kilogiram 30 a cikin kowace ganga.

A wata sanarwa da Mahmud Isa Yola, Hadimin Shugaban NDLEA a kan Kafofin Sadarwa ya sa wa hannu, ta ce, asalin dai an tare ƙwayoyin ne a kan hanyarsu ta zuwa wurin mai su, Fasto Anietie Okon Effiong, wanda aka kama a wani samame da aka kai a bakin tekun Oron a Oron. Faston dai ya yi nufin kai ƙwayoyin ne zuwa Jamhuriyar Kamaru.

Wannan na zuwa ne bayan kama wasu miyagun ƙwayoyi guda huɗu da nauyinsu ya kai kilogiram 4.074 da aka yi yunƙurin tura su ƙasashen Australia, Indonesia da Philippines, tare da safarar wiwi mai nauyin kilogiram uku da ta nufi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a wasu kamfanonin jigilar kayayyaki a Legas.

A ɗaya ɓangaren kuma, a Sakkwato, an kama wani soja mai shekaru 90 mai ritaya, Usman Adamu a ranar Laraba 3 ga watan Agusta a Mailale, Ƙaramar Hukumar Sabon Birni bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

An kama wanda ake zargin ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.1.

A filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas kuwa wani ne ɗan shekara 37 ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Ovia, Jihar Edo, kuma mazaunin ƙasar Italiya, Solo Osamede, wanda aka kama da laifin haɗiye sinƙi 41 na tabar heroin don ya fitar da shi ta jirgin Turkish Airline zuwa Milan, Italiya ta Istanbul, Turkiyya a ranar Asabar 30 ga Yuli.

Biyo bayan kama shi, tare da tsare shi da aka yi, Osamede ya fitar da abin da ya haɗiye a ofishin NDLEA.

Haka zalika, an kama wata motar fasinja Jatau Lydia Lami a filin jirgin sama na Legas bisa yunƙurin fitar da Tramadol mai ƙarfin 225 guda 1,700 da aka ɓoye a cikin jakunkunanta zuwa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya ta jirgin Turkish Airline a ranar Lahadi 31 ga watan Yuli.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wacce ake zargin, mai ‘ya’ya uku, ‘yar asalin Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ce ta jihar Kaduna, kuma tana zaune a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya, tare da iyalanta.

Da ake bincikenta, ta ce ta ɗauki matakin hakan ne a kan matsin lamba na neman kuɗin fansa Naira miliyan 5 don kuɓutar da mahaifiyarta daga hannun ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da ita tun watan Yuni.

Haka zalika a filin jirgin saman SAHCO na fitar da kaya, an daƙile yunƙurin da wasu jami’an dakon kaya suka yi na fitar da tabar wiwi guda biyu a cikin haɗakar kaya zuwa Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ranar Alhamis 4 ga watan Agusta, inda jami’an Hukumar NDLEA suka kama biyu daga cikinsu a wani samame da suka yi. Mutanen sun haɗa da: Oladipupo Oladapo Fatai da Animashaun Qudus, yayin da wasu biyu ke hannunsu.

A Zamfara, jami’an NDLEA a ranar Alhamis 4 ga watan Agusta, sun kama wata babbar mota daga Benin, Jihar Edo ta nufi Sakkwato ɗauke da Diazepam guda 50,000 mallakin wani dillalin ƙwayoyi, Umaru Attahiru.

A Kogi kuma aka kama buhu 14 ɗauke da kwalabe 1,376 na maganin Codeine mai nauyin kilogiram 190.4.

An kama su ne a hanyar Okene zuwa Abuja a ranar Laraba 3 ga watan Agusta. Wani bincike da aka gudanar a Abuja a ranar ya kai ga cafke Jude Ikenna da Ozoemene Cornelius.

A Kaduna, mutum huɗu da ake zargi: Sulaiman Rabi’u; Sanusi Sha’aibu; Ma’aruf Habibu da Christian Nnachor, sun shiga hannun Hukumar ta NDLEA a jihar.

An kama su ne a Zariya ɗauke da Tramadol 225mg guda 106,770, Diazepam, Exol-5 da kwalabe 100 na maganin tari na Codeine.

A Jihar Enugu, an gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 143.5 a cikin wasu shaguna da aka kulle a sabuwar kasuwar jihar a ranar Asabar 6 ga watan Agusta, yayin da kuma a Delta, an kama wani da ake zargi mai suna Ike Okparachi mai shekaru 42 a Abraka Junction, Asaba ɗauke da Tramadol 10,550. 225mg; Swinol; Rohypnol; da kwalabe 3,105 na codeine da kuma giram 69 na Molly.

Shugaban Hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya yaba wa hafsoshi da jami’an hukumar ta Akwa Ibom, MMIA, Sakkwato, Zamfara, Kogi, Delta, Enugu, Kaduna kwamandojin hukumar da kuma Daraktan Ayyuka da Bincike na DOGI bisa hazaƙar da suka nuna.

Ya kuma buqace su da sauran jami’an hukumar a duk faɗin Nijeriya da su qara kaimi da lura yayin gudanar da ayyukansu.