
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi murabus daga muƙaminsa domin neman takarar gwamna a jihar Oyo a yayin zaɓen 2027.
A wasiƙar murabus ɗin da ya fitar mai kwanan wata 22 ga Afrilu, 2026, wadda ya aike wa Shugaba Bola Tinubu, Adelabu ya bayyana cewa wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Afrilu, 2026, domin bada sararin miƙa ragamar yadda ya dace.
Ya bayyana cewa ya sauka ne tare da matuƙar girmamawa da godiya ga Shugaba Bola Tinubu da ya naɗa shi a muƙamin.
“Na rubuta wannan wasiƙa ne tare da girmamawa da godiya don sanar da murabus ɗina daga muƙamin Ministan Lantarki na Tarayyar Nijeriya”, inji shi.
Ya kuma jaddada godiyarsa ga shugaban bisa damar da ya ba shi na yin aiki, inda ya bayyana naɗin nasa a matsayin wata alfarma.
Ya ƙara da cewa, ya kasance babban abin alfarma a gare shi wajen bayar da gudunmawa ga cigaban ƙasa da kuma aiwatar da gyare-gyare a fannin lantarki, wanda shi ne ginshiƙin ci-gaban masana’antu da sauyin lamuran tattalin arziƙin ƙasa.

